Annobar Corona: Babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Ministar kudi

Annobar Corona: Babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Ministar kudi

Hasashe da bincike na tsimi da tanadi da hukumar kiddiga ta Najeriya ta gudanar ya nuna tattalin arzikin Najeriya zai shiga halin tabarbarewa da kashi -4.4 saboda annobar Coronavirus.

Premium Times ta ruwaito ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labaru bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya yi bayani game da yadda ake Sallar Idin mutum 1 a gida

“Hukumar kididdig ta gudanar da bincike, kuma sakamakon binciken ya nuna tattalin arzikin Najeriya za ta shiga mawuyacin hali, za ta fadi da kashi -4.4,

"Amma duba da aikin da kwamitin tayar da komar tattalin arzikin kasa take yi, muna sa ran zamu rage radadin faduwar tattalin arzikin.

“Idan muka dabbaka duk shawarwarin da aka bayar, faduwar tattalin arzikin zai ragu da kashi -0.4, duk dai yadda aka yi sai mun fuskanci tabarbarewar tattalin arziki, kokarin da muke yi shi ne mu tabbata faduwar ba ta yi zurfi ba, ta yadda da zarar an shiga 2021 zamu farfado.” Inji ta.

Annobar Corona: Babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Ministar kudi
Ministar kudi Zainab Ahmad Hoto: Pulse
Asali: Twitter

Najeriya na cikin kasashen da suka fi fuskantar matsala sakamakon annobar Corona saboda babbar hanyar samun kudinta shi ne sayar da man fetir, wanda a yanzu darajarsa ta karye.

Karyewar darajar man na nufin kudin shigar kasar sun ragu kenan, haka zalika ga shi kasar ta dakatar da duk wasu harkokin kasuwanci saboda gudun yaduwar annobar.

Hakan ya sa dole Najeriya ta sake bude kasuwanci duk da cigaba da ruruwar cutar Coronavirus a kasar, kamar yadda minista Zainab ta yi bayani.

“Muna cikin mawuyacin hali, kalubalen da muke fuskanta guda biyu ne, akwai matsalar kiwon lafiya, akwai kuma matsalar tattalin arziki, koda muke kokarin shawo kan matsalar kiwon lafiya, dole kuma mu lura da yadda zamu tallafa ma tattalin arzikin kasar don gudu rugujewar ta.

“Dole mu ciyar da jama’a, amma babu yadda za’a ciyar da jama’a ba tare da an yi noma a gona ba, muna da yawan jama’a don haka bamu son shiga hatsari, kuma bamu da isashshen abinci da zai rage radadin matsalar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel