Da duminsa: An samu karin mutum 284 dauke da korona, jihohin Legas, Rivers da Oyo ke kan gaba

Da duminsa: An samu karin mutum 284 dauke da korona, jihohin Legas, Rivers da Oyo ke kan gaba

Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya ta bayyana, a yau 20 ga watan Mayun 2020, an samu karin mutum 284 dauke da cutar korona a fadin kasar nan.

Jihar Legas na da mutum 199 da aka tabbatar suna dauke da cutar yayin da jihar Rivers ke biye da ita da mutum 26.

Jihar Oyo na da mutum 19 da aka tabbatar suna dauke da cutar yayin da babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, da jihar Borno ke da takwas-takwas.

Jihar Filato da ke arewacin Najeriya na da mutum bakwai, jihar Jigawa na da mutum shida sai kuma babbar cibiyar kasuwancin arewa, wato jihar Kano na da karin mutum biyar.

Jihar Abia na da mutum biyu sai jihohin Ekiti, Delta, Kwara da Taraba da ke da mutum daddaya.

A yau dai jimillar masu cutar korona a fadin Najeriya ya kai 6,677. Mutum 1,840 ne suka warke garas kuma aka sallamesu daga asibiti yayin da aka rasa rayuka 200 sanadiyyar annobar da ta game duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel