Manyan ofishoshin gwamnatin tarayya 5 da akayi gobara cikin wata 1

Manyan ofishoshin gwamnatin tarayya 5 da akayi gobara cikin wata 1

Makonni bakwai da suka gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a birnin tarayya Abuja, jihar Legas da na Ogun domin takaita yaduwar sabuwar cutar Coronavirus.

Wannan doka ya shafi dukkan ma'aikatan gwamnati inda aka umurci dukkan ma'aikata dake kasa da daraja ta 15 a aikin gwamnati da suyi zamansu a gida.

Tun daga lokacin hedkwata-hedkwata da manyan ma'aikatu suka fara fuskantar gobara a birnin tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa ta kawo muku jerin ofishoshin gwamnati biyar da suka zalzala cikin wata daya.

1. Ofishin akawunta janar (Gidan baitul mali)

A ranar 8 ga Afrilu, 2020, Ginin da aka fi sani da 'Gidan baitul mali' wato Treasury House' na kusa da hedkwatar hukumar yan sandan Abuja, a unguwar Garki ya yi gobara.

Karamin ministan kasafi da tsare - tsare na kasa, Prince Clem Agba, ya yi magana a kan gobarar da ta tashi a ofishin babban akawu na kasa inda ake zargin ta tafka barna a ginin ofishin na akawun gwamnatin tarayya.

2. Hedkwatar hukumar CAC

A ranar 15 ga Afrilu, Gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.

Gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.

Manyan ofishoshin gwamnatin tarayya 5 da akayi gobara cikin wata 1
Hoto daga Ofishin CAC
Source: Twitter

3. Hedkwatar INEC dake Abuja

A ranar 17 ga watan Afrilu, Hedkwatar hukumar gudanar da zabe ta kasa watau INEC dake birnin tarayya Abuja ya ci da wuta.

Manyan ofishoshin gwamnatin tarayya 5 da akayi gobara cikin wata 1
gobara cikin wata 1 Ofishn INEC
Source: Twitter

4. Ofishin babban bankin Najeriya CBN

A ranar 21 ga Afrilu, an samu gobara a ofishin babban bankin Najeriya CBN, reshen Jos, jihar Plateau. Bankin ta tabbatar da hakan a shafinta na Tuwita inda ta bayyana cewa tuni an kashe wutar.

5. Hedkwatar NIPOST

A ranar 20 ga watan Mayu, 2020, Mumunar gobara ya auku a hedkwatar hukumar ayyukan aika da karban sako watau NIPOST dake birnin tarayya Abuja.

Rahoto ya bayyana cewa gobarar ta fara ci ne tun karfe 9 na safiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel