Sanwo-Olu: Mun kusa bude dakunan ibada da wuraren kasuwanci a Legas

Sanwo-Olu: Mun kusa bude dakunan ibada da wuraren kasuwanci a Legas

Mai girma gwamna Babajide Sanwo-Olu ya shaidawa jama’ansa cewa kwanan nan gwamnatin Legas za ta bude gari domin a cigaba da kasuwanci da sauran harkokin yau da kullum.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a jiya Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2020. Ya ce dole dakunan ibada da wuraren kasuwanci su cika wasu sharuda kafin a bada damar sake bude su.

Jaridar The Nation ta ce mista Babajide Sanwo-Olu ya yi wannan bayani ne a gidan gwamnati da ke Marina, garin Ikeja. Gwamnan ya saba yi wa mutanensa bayanin halin da su ke ciki.

“Mu na duba da la’akari da yadda za a cire takunkumun zaman-gida. Idan mun ga cewa jama’a su na bin doka, to za a iya yin wannan a cikin makonni biyu zuwa uku.” Inji Sanwo-Olu.

Mai girma gwamnan ya cigaba da fadawa mutanensa: “Idan ba haka ba, zai iya daukar kamar wata guda zuwa biyu. Sai mun tabbatar cewa kowa zai bi sharudan da mu ka kafa.”

Mista Sanwo-Olu ya sanar da cewa kwanaki an samu wasu ma’aikatan gidan gwamnati goma da su ka kamu da cutar Coronavirus a Legas. Duk da haka ana tunanin bude ko ina a jihar.

KU KARANTA: Masu fama da Coronavirus a Legas sun karu da mutum 177, adadi ya kai 2550

A wani bincike da kungiyar ‘yan kasuwa na jihar Legas ta yi, an gano cewa takunkumin kullen da gwamnati ta kakaba a Legas ya taba 81% na hanyoyin neman abincin mutanen da ke jihar.

Kashi 17% na ‘yan kasuwan jihar Legas ne wannan doka ta zaman gida ba ta yi wa mummunan illa ba. Wannan ya sa ake kiran gwamnati ta budewa mutane hanyoyin neman kudinsu.

A cewar gwamnan, za a kawo tsare-tsare domin a rika bibiyar yadda ake bin sharudan da aka sa. Gwamnan ya ce akwai matakan da za a bi kafin a kai ga bude wuraren kasuwanci da ibadu.

Za a rika bibiyar har wuraren cin abinci domin a tabbatar da bin doka. Dakunan biki, manyan shaguna da sauran wuraren za su yi rajista da gwamnatin jiha kafin a ba su damar budewa.

Ya ce: “Haka zalika, za mu yi aiki da dakunan ibada domin mu ga irin shirin da su ka yi na bada tazara da amfani da kariyar fuska wurin bauta, saboda lokacin da za mu tashi bude su.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel