Boko Haram: Yadda dakarun sojin sama suka ragargaza 'yan ta'adda a Sambisa

Boko Haram: Yadda dakarun sojin sama suka ragargaza 'yan ta'adda a Sambisa

Rundunar sojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole ta ragargaza mayakan Boko Haram a dajin Sambisa da ke Borno a ranar 15 ga watan Mayun 2020.

Kamar kamar yadda takardar da shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche ya fitar, sun kai harin ne bayan bayanan sirri da suka samu a kan al'amuran 'yan ta'addan.

Ya ce dakarun sojin saman sun yi amfani da jiragen saman yaki wajen ragargaza 'yan ta'addan, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Enenche ya yi bayanin cewa ta jirgin yakin ne suka hango wurin zaman 'yan ta'addan.

Ya ce jiragen saman dakarun sojin sun dinga sakin bama-bamai a yankin, sun yi nasarar halaka wasu daga ciki tare da tarwatsa makamansu.

Boko Haram: Yadda dakarun sojin sama suka ragargaza 'yan ta'adda a Sambisa
Boko Haram: Yadda dakarun sojin sama suka ragargaza 'yan ta'adda a Sambisa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kano: Akwai yuwuwar hauhawar yawan masu korona babu dadewa- Ganduje

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce akwai yuwuwar hauhawar yawan masu cutar coronavirus a jihar Kano bayan samar da karin dakunan gwajin cutar a jihar.

Ganduje ya sanar da hakan ga manema labarai a yayin ganawa da kwamitin dakile yaduwar cutar coronavirus na Kano a ranar Juma'a, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce an kammala shirin samar da dakunan gwaji a kananan hukumomi 36 da ke da nisa da birnin Kano.

"Za mu bude cibiyoyin gwaji a dukkan kananan hukumomi 36 da ke da nisa da birni. Za mu ci gaba da shiri, dole ne mu dauka matakan gaggawa.

"Za mu tabbatar da cewa da cewa dukkan ma'aikatun jihar nan na shirye koda irin wannan halin ko-ta-kwana ya taso," yace.

Ya kara da cewa za su kara kokari wajen tabbatar da an fatattaki annobar kwata-kwata.

Ganduje yace mulkin sa zai ci gaba da wayar wa jama'ar jihar Kano kai tare da sauran tsare-tsaren yaki da annobar.

Ya yi kira ga ma'aikatan lafiya da su mayar da hankali wajen kula da sauran mutane masu cutukan da ba korona ba.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta horar da daruruwan ma'aikatan lafiya don yakar annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel