Boko Haram: NAF za ta kara dakarunta a yankin arewa maso gabas din Najeriya

Boko Haram: NAF za ta kara dakarunta a yankin arewa maso gabas din Najeriya

Shugaban dakarun sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, ya bayyana cewa rundunar sojin saman Najeriya za ta kara yawan dakarunta a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

Kamar yadda shugaban ya bayyana, rundunar za ta yi hakan ne don kokarin ganin karashen halaka Boko Haram a yankin.

Ya bada wannan tabbacin ne a jiya, yayin ziyarar da ya kai ta kaddamar da wasu ayyuka a hedkwatar sojin saman ta rundunar Operation Lafiya Dola a Maiduguri.

Ya jinjina wa kokarin rundunar na kammala ayyuka 889 a cikin wata ukun farko na shekarar nan wanda suka yi shi don murkushe ragowar 'yan ta'addan.

"Matasalar tsaro babban kalubale ne ga ci gaban mu. Dole ne mu tabbatar da kawo karshen sa. Ina farin cikin ganin ci gaban da ake samu yayin yaki da 'yan ta'addan.

"Na yi farin cikin ganin yadda sojin saman suka yi aiki a sama na sa'o'i 1690, ayyuka 889 da kuma tarwatsa mafakar 'yan ta'adda 33 a cikin watanni uku na farkon 2020.

"Zamu jinjina musu ta hanyar tabbatar da walwalar su ce kan gaba a komai.

"Rundunar sojin saman za ta ci gaba da kokari. Wasu daga cikin abubuwan da za mu kaddamar sun hada da karin ma'aikata don karasa 'yan ta'addan da suka rage," yace.

Boko Haram: NAF za ta kara dakarunta a yankin arewa maso gabas din Najeriya
Boko Haram: NAF za ta kara dakarunta a yankin arewa maso gabas din Najeriya. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kashe-kashen 'yan bindiga: Yadda dan majalisa ya fashe da kuka a yayin zaman majalisa

A wani labari na daban, mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Tafoki ya samu damar yi wa zauren majalisa jawabi amma sai ya fashe da kuka a kan rashin tsaron da ya addabi mazabar Faskari.

Yankunan sun saba samun hare-haren 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk wani nau'in rashin tsaro.

A makon da ya gabata, mutum biyar suka halaka sakamakon hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Tafoki, wanda ke wakiltar mazabar Faskari a majalisar jihar, ya ce ba a samun rana daya a halin yanzu da za ta wuce ba tare da an ji harin da aka kai yankin ba.

Kamar yadda yace, karamar hukumar Faskari a halin yanzu za a iya kwatanta ta da Maiduguri, "Ko a daren jiya 'yan bindiga sun kai hari garin Daudawa inda suka yi garkuwa da mutum 4 sannan suka raunata wasu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel