Ranar ma’aikata: Ba za mu yarda a zaftare albashin ma’aikata da sunan Coronavirus ba – NLC

Ranar ma’aikata: Ba za mu yarda a zaftare albashin ma’aikata da sunan Coronavirus ba – NLC

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ya gargadi gwamnati da ma’aikatu game da dakatar da albashin ma’aikata da sunan annobar Coronavirus, ko kuma zaftare musu albashi.

Daily Trust ta ruwaito shugaban NLC, Ayuba Wabba ne ya sanar da haka a ranar Talata cikin wata sanarwa da ya fitar don tunawa da ranar ma’aikata da ta duniya na shekarar 2020.

KU KARANTA: Majalisa ta amince ma Buhari ya sake antayo ma Najeriya bashin N850,000,000,000

Wabba ya yi kira ga NLC na kowace jaha da ta yi tirjiya ga duk wani yunkurin gwamnati da ma’aikatu na zaftare albashin ma’aikata, saboda a cewarsa ba yanzu bane lokacin rage albashi.

“Muna tabbatar ma ma’aikata cewa babban abin da muka sa a gaba shi ne farfado da tattalin arziki domin su koma bakin aikinsu, mun mayar da hankulanmu ga inganta albashin ma’aikata, dawo da ma’aikatan da suka rasa ayyukansu.” Inji shi.

Ranar ma’aikata: Ba za mu yarda a zaftare albashin ma’aikata da sunan Coronavirus ba – NLC
Wabba
Asali: Depositphotos

Sai dai Wabba yace duba da halin da ake ciki na annobar Coronavirus, ba za’a gudanar da bikin tunawa da ranar ma’aikata kamar yadda aka saba ba.

“Za mu samar da hanyoyin da ma’aikatan Najeriya za su samu sakon mu na shekarar 2020, muna kira ga ma’aikata su tuntubi babban ofishin NLC idan har aka musu wani rashin adalci da ya shafi COVID-19.

“Yayin da muke sa ran ganin karshen wannan ibtila’i, ya dace mu cigaba da kula, mu zauna a gida, kuma mu kasance cikin aminci.” Inji shi.

A yanzu haka ma’aikatu masu zaman kansu sun aika ma’aikatansu hutu ba tare da biyansu albashin ko sisi ba, yayin da wasu kuma suka rage albashin ma’aikatan nasu.

Kwalejin horas da matuka jirgin sama dake garin Ilorin ta sanar da rage kashi 10-42 na albashin ma’aikatanta na watan Afirlu, amma banda masu amsan N80,000 kasa.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kano ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar a makon da ta gabata.

A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.

Gwamnatin ta gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel