An sake samun bullar Coronavirus a Katsina, Masari ya garkame karamar hukumar Safana

An sake samun bullar Coronavirus a Katsina, Masari ya garkame karamar hukumar Safana

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya garkame karamar hukumar Safana babu shiga babu fita sakamakon samun bullar annobar Coronavirus a garin.

Sakataren gwamnatin jahar, Mustapha Inuwa ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, inda yace dokar za ta fara aiki ne daga karfe 7 na safiyar Asabar, 25 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Corona: Kotun tafi da gidanka ta kama mutane 500 da laifin karya dokar ta baci a Abuja

Inuwa yace gwamnati ta dauki matakin ne bayan sakamakon gwaji da hukumar NCDC ta gudanar ya tabbatar da kamuwar wasu mutane uku a Safana da cutar Coronavirus.

“Bincike ya nuna dukkanin mutanen da suka kamu da cutar sun yi mu’amala da mutumin da nan da aka samu da ita a karamar hukumar Dutsanma, don haka garkame karamar hukumar yayi daidai da shawarar gwamnati da masu ruwa da tsaki na garkame duk inda aka samu bullar cutar.” Inji shi.

Don haka, ya yi kira ga al’ummar Safana su baiwa gwamnati hadin kai wajen yin biyayya ga dokar saboda jami’an tsaro na tafe domin tabbatar da jama’a sun bi dokar sau da kafa.

“Kamar yadda aka saba, gwamnan ya umarci kwamitin yaki da yaduwar cutar COVID-19 a Katsina ta gano kayan hatsi da magunguna da ake bukata a yankin domin basu daman gudanar da cinikin saya da sayarwa na dan wani lokaci.” Inji shi.

An sake samun bullar Coronavirus a Katsina, Masari ya garkame karamar Safana

An sake samun bullar Coronavirus a Katsina, Masari ya garkame karamar Safana
Source: Twitter

Daga karshe ya nemi jama’a su yi amfani da daman azumin Ramadan wajen gudanar da addu’o’i ga Allah domin Ya sawwake wannan annoba da ta dabaibaye duniya.

A yanzu haka gwamnatin ta garkame kananan hukumomin Daura, Katsina, Dutsanma, Batagarawa, Mani, Jibia da kuma Safana, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

A wani labarin kuma, Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya sanar da garkame wuraren bauta, wuraren taron jama’a da kasuwanni a kokarinsa na dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ma al’ummar jahar jawabi a ranar Alhamis, inda yace ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Gwamnan yace sun tattauna matsalar yaduwar cutar a jahar da sauran matsalolin kiwon lafiya a suka dabaibaye al’ummar jahar. A yanzu akwai mutane 8 dake dauke da cutar a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel