Covid-19: An fara gwada riga-kafin cutar Korona a kan mutum 2

Covid-19: An fara gwada riga-kafin cutar Korona a kan mutum 2

- An fara gwada riga-kafin cutar Covid-19 a Oxford da ke Birtaniya a kan wasu mutum biyu

- An fara yi musu allurar don suna daga cikin mutum 800 da aka zaba domin yin gwajin riga-kafin

- Amma kuma, rabi daga cikin mutum 800 din za a yi musu allurar riga-kafin cutar Covid-19 ne inda sauran za a yi musu ta kariya daga cutar Sankarau

An fara gwada riga-kafin cutar Covid-19 a Oxford da ke Birtaniya a kan wasu mutum biyu.

An fara gwajin riga-kafin cutar ne a kan wasu mutum biyu 'yan sa-kai. An fara yi musu allurar don suna daga cikin mutum 800 da aka zaba domin yin gwajin riga-kafin.

Amma kuma, rabi daga cikin mutum 800 din za a yi musu allurar riga-kafin cutar Covid-19 ne inda sauran za a yi musu ta kariya daga cutar Sankarau.

Wadanda aka yi musu allurar, ba za su san ta wacce cutar aka yi musu ba, amma likitocin za su tantance.

Covid-19: An fara gwada riga-kafin cutar Korona a kan mutum 2
Covid-19: An fara gwada riga-kafin cutar Korona a kan mutum 2
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: FG ta yi magana a kan halin da jihar Kano ke ciki

A wani labari na daban, Kwamitin shugaban kasa na yakar cutar Covid-19 ya ce yadda masu cutar ke karuwa a jihar Kano na ci gaba da tada musu hankali.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja a jiya yayin jawabi ga kwamitin.

Ya ce: "Halin da jihar Kano ke ciki abin tada hankali ne. Kwamitin na ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar don shawo kan lamarin.

"Kwamitin ya gano cewa ana ci gaba da samun masu cutar a kasar nan. Wannan kuwa ya danganta ne da yadda aka fadada wuraren gwajin."

Mustapha ya kara da cewa, ganin yadda lamarin ya sake yawaita, sun sauya sabbin tsarin gwaji don yanzu gida-gida ake bi don yin gwajin a jihohin Legas da Abuja.

Kamar yadda yace, gwaji, tantancewa, killacewa da kula da masu cutar ya zama dole in har ana bukatar takaita yawan masu kamuwa da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel