Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19

Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19

Tun bayan bullar cutar Covid19 a birnin Wuhan da ke kasar China a karshen shekarar 2O19, cutar ta cigaba da bazuwa a duniya kamar wutan dare inda ta ke ta kashe mutane da dama.

Hakan ya faru ne saboda rashin takamammen magani ko rigafi na kwayar cutar duba da cewa sabuwar cuta ce da ba a taba ganin ta a duniya ba.

Ana ta gwaje gwajen magunguna da dama a kasashen duniya daban daban amma kawo yanzu ba a cimma gano takamemen magani ko rigakafi da hukumar lafiya ta duniya ta amince da ingancin shi ba.

Bullar cutar ya kawo sauye sauye a yadda kasashe ke gudanar da harkokin baki daya inda mafi yawanci kasashe suka rufe iyakokin su tare da saka dokar kulle a birane da dama ciki har da Najeriya.

Duk da cewa cutar ta kashe mutane da dama, akwai wasu mutanen da suka kamu amma daga bisani suka warke da taimakon likitoci.

Ga dai kiddigan kasashe 1O da cutar ta kama mutane tare da adadin wanda suka warke da kuma wadanda suka riga mu gidan gaskiya zuwa ranar 23 ga watan Afrilu kamar yaddda Tracking meters ta wallafa.

1. Amurka

Wandanda suka kamu - 849,092

Wadanda suka mutu - 47,681

Wadanda suka warke - 84,050

2. Spain

Wandanda suka kamu - 208,389

Wadanda suka mutu - 21,717

Wadanda suka warke - 85,915

3. Italy

Wandanda suka kamu - 187,327

Wadanda suka mutu - 25,085

Wadanda suka warke - 54,543

4. Faransa

Wandanda suka kamu - 159,877

Wadanda suka mutu - 21,340

Wadanda suka warke - 40,657

DUBA WANNAN: Kano: Ganduje ya yi magana a kan dage dokar hana zirga-zirga

5. Jamus

Wandanda suka kamu - 150,648

Wadanda suka mutu - 5,315

Wadanda suka warke - 103,300

6. Burtaniya

Wandanda suka kamu - 133,495

Wadanda suka mutu - 18,100

Wadanda suka warke - Ba a san adadin ba

7. Turkiyya

Wandanda suka kamu - 98, 674

Wadanda suka mutu - 2,376

Wadanda suka warke - 16,477

8. Iran

Wandanda suka kamu - 85,996

Wadanda suka mutu - 5,391

Wadanda suka warke - 63,113

9. China

Wandanda suka kamu - 82,798

Wadanda suka mutu - 4,632

Wadanda suka warke - 77,207

10. Rasha

Wandanda suka kamu - 57,999

Wadanda suka mutu - 513

Wadanda suka warke - 4,420

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel