COVID-19: An damke mutum 2 da ake zargi da yunkurin yada cutar coronavirus

COVID-19: An damke mutum 2 da ake zargi da yunkurin yada cutar coronavirus

A ranar Alhamis ne kasar Tunisia ta bayyana cewa ta damke wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin shafawa jami'in tsaro cutar coronavirus.

An zargi daya daga cikinsu wanda dan ta'adda ne da amfani da karfinsa wajen janyo mutane duk da kuwa yana dauke da cutar coronavirus, ma'aikatar cikin gida ta sanar.

Dayan wanda ake zargin kuwa an saka mishi sharudda tsaurara tare da umartarsa a kan ya dinga zuwa ofishin 'yan sanda kullum, ya ce da gangan yake tarin don shafawa mutane cutar.

Ana kara bincikar lafiyar mutane biyun da ake zargi da yunkurin yada cutar.

An kama mutum biyun ne a ranar Litinin a Kebili da ke kudancin kasar Tunisia, kamar yadda mai magana da yawun Houssem Eddine Jebabili ya sanar.

Kasar Tunisia wacce aka samu daruruwan mutane dauke da cutar, na cikin halin ko ta kwana ne tun a 2015 bayan hare-haren 'yan ta'adda.

COVID-19: An damke mutum 2 da ake zargi da yunkurin yada cutar coronavirus
COVID-19: An damke mutum 2 da ake zargi da yunkurin yada cutar coronavirus
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu

A wani labari na daban, wani mutum mai fama da cutar coronavirus sun ba hammata iska tare da wani jami'in NSCDC a cibiyar killace masu cutukan da ke yaduwa ta Kaduna.

Damben ya biyo bayan hana majinyacin tserewa da jami'in NSCDC din yayi daga cibiyar.

Majinyacin wanda aka sakaya sunansa, ya hari Joshua Philip ne bayan yana gadin cibiyar kuma ya hana shi fita da zummar zai sha iska daga waje.

Kamar yadda takardar da mataimaki na musamman ga shugaban NSCDC din a fannin yada labarai, Ekuna Gbenga ya fitar, an kara tsananta tsaro a farfajiyar cibiyar don gujewa sake faruwar lamarin.

Takardar ta ce,"Wani mai fama da cutar coronavirus ya yi yunkurin tserewa daga cibiyar killacewa ta Kaduna.

"An ba hammata iska tsakaninsa da jami'in hukumar NSCDC bayan majinyacin yayi yunkurin amfani da karfi wajen kwatar makullin kofar don ficewa.

"Majinyacin kuwa ya dage wajen dambe da jami'in bayan ya hana shi fita daga cibiyar. Wannan lamarin kuwa yasa aka killace jami'in.

"Tuni dai aka saka wa mabudin sinadaran kashe kwayoyin cuta sannan aka bai wa jami'in wasu magunguna. An umarceshi da ya killace kansa na makonni biyu sannan ya kira cibiyar idan ya ga wata alama.

"A halin yanzu dai an kara inganta tsaro a cibiyar killacewar don gudun sake aukuwar lamarin," takardar tace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel