'Yan sanda sun damke matar da tayi wa hadimarta tsarki da tozali da barkano

'Yan sanda sun damke matar da tayi wa hadimarta tsarki da tozali da barkano

- Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta damke wata tsohuwa mai shekaru 75 wacce ake zargi da duka tare da zuba barkono a ido da gaban mai aikinta

- Mai aikin mai suna Chidinma ta ce an dauko ta ne daga Ohaji Egbema da ke jihar Imo kusan watanni 12 da suka gabata

- Chidinma ta sanar da jaridar The Nation cewa, matar ta saba gayyatar bata-gari don dukanta a duk lokacin da ta bata mata rai

Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta damke wata tsohuwa mai shekaru 75 wacce ake zargi da duka tare da zuba barkono a ido da gaban mai aikinta.

Makwabtan matar mai suna Comfort Obi ne suka mika ta gaban ofishin 'yan sanda da ke Ekumenyi a Abakaliki sakamakon tsananin zaluntar mai aikinta da take yi.

Ta farfasawa mai aikin jiki sakamakon tsananin dukan da take mata.

Mai aikin mai suna Chidinma ta ce, an dauko ta ne daga Ohaji Egbema da ke jihar Imo kusan watanni 12 da suka gabata.

An kaita wajen Comfort Obi ne don tayata ayyukan gida kuma ana biyanta.

Bincike ya nuna cewa, Chidinma ta fara aikatau ne bayan mutuwar mahaifiyarta da makantar mahaifinta wanda nauyin 'yan uwanta hudu yake kansa.

Chidinma ta sanar da jaridar The Nation cewa, matar ta saba gayyatar bata-gari don dukanta a duk lokacin da ta bata mata rai.

'Yan sanda sun damke matar da tayi wa hadimarta tsarki da tozali da barkano

'Yan sanda sun damke matar da tayi wa hadimarta tsarki da tozali da barkano
Source: Facebook

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai wa Buratai hari har sansanin Ngamdu

Ta ce a duk lokacin da ta dauka biskit da ruwan lemu na matar bayan ta barta da yunwa, tana watsa mata barkono a gabanta da idanunta.

Osita Ezechukwu makwabcinsu ne wanda ya garzaya ofishin 'yan sanda don gudun kada ayi kisan kai a kusa dasu.

Ya ce ba sau daya ba ya ke jan kunnen matar a kan ta gujewa cin zarafin mai aikin. Ya ce baya ga duka, tana ba mai aikin aiki mai matukar wahala.

Matar tace duk da tayi nadamar abinda tayi, sai da ta nemi izinin kanwar mahaifin mai aikin kafin ta watsa mata barkono a gaba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Ta ce an bayar da belin wacce ake zargin, ita kuwa mai aikin an dubata a asibiti tare da mika ta ga iyayenta.

Ta kara da cewa za a gurfanar da wacce ake zargin bayan annobar Coronavirus ta wuce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel