COVID-19: Lauyoyi sun yi gudun ceton rai bayan wanda ake zargi ya yi tari a kotu

COVID-19: Lauyoyi sun yi gudun ceton rai bayan wanda ake zargi ya yi tari a kotu

- Wata karamar dirama ta auku a cikin zauren kotun majistare da ke Osogbo a jihar Ogun

- Wanda ake zargi ne ya yi tari yayin da ake shari'a, lamarin da yasa lauyoyi uku suka tsere

- Alkalin kotun kuwa ya bayyana cewa komai tarin da wanda ake zargin zai yi, ba za a daina shari'ar ba

An samu wata kamar dirama a cikin wata kotun majistare dake jihar Osun.

Wani wanda ake zargi da cin zarafi ne ya yi tari yayin da ake karanto mishi laifukansa.

Wannan ci gaban kuwa ya kawo tangarda a shari'ar don kuwa lauyoui uku ne suka gaggauta tserewa.

Duk da faruwar wannan lamarin kuwa, mai shari'a Olusegun Ayilara ya sanar da wanda ake zargin cewa tarinsa ba zai tsayar da abinda ake yi ba.

An gurfanar da Ige ne tare da wani mai suna Rasaq Sunday, Wasiu Adeyanju da Samson Ogunleye.

Ana zargin cewa a ranar 6 ga watan Afirilun 2020 a titin Olugun da ke Osogbo, sun hada kai wajen aikata laifi wanda ya ci karo da sashi na 516 na dokokin laifukan jihar Osun na 2002.

COVID-19: Lauyoyi sun yi gudun ceton rai bayan wanda ake zargi ya yi tari a kotu
COVID-19: Lauyoyi sun yi gudun ceton rai bayan wanda ake zargi ya yi tari a kotu
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kano za ta rufe wasu kasuwannin jihar

An zargesu da yin amfani da fasassun kwalabe, almakashi da adda wajen raunata wani mai suna Lateef Kareem.

Rasaq Olayiwola ne ya sanar da bayyanar masu gurfanarwar.

Wanda ake zargin wanda bashi da lauya, ya musanta zargin da ake masa.

Alkalin kotun, Ayilara, ya bada belin wanda ake zargin a kan N200,000 da kuma tsayayye daya.

Ya dage sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Maris.

A wani labari na daban, wani jinjiri a garin Saharanpur da ke Uttar Pradesh a kasar India, an sa mishi suna 'Sanitizer'.

Iyayen sun ce sun yi hakan ne don tunatar dasu irin halin da duniya ta taba shiga.

A yayin zantawa da manema labarai, Omveer, mahaifin jaririn ya ce yana jinjinawa gwamnati da yadda take kokarin shawo kan barkewar annobar Coronavirus a kasar, jaridar IndiaToday ta ruwaito.

"Ni da mata ta muna jinjinawa matakan da firayim minista Narendra Modi da babban minista Yogi Adityanath suka dauka a kan cutar," yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel