Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi

Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi

- Kasar Najeriya da jamhuriyar Chadi a ranar Alhamis sun amince da jaddada yarjejeniyar yakar Boko Haram da ke tsakaninsu

- Manjo janar Bashir Magashi mai murabus, ya sanar da hakan ne a taron da aka yi tsakanin hukumomin kasashen biyu a Abuja

- Ministan tsaro na kasar Chadi, Mahamat Aba-Ali Soilah ya yi alkawarin bada goyon baya a kan wannan lamarin

Kasar Najeriya da jamhuriyar Chadi a ranar Alhamis sun amince da jaddada yarjejeniyar yakar Boko Haram da ke tsakaninsu.

Ministan tsaro, Manjo janar Bashir Magashi mai murabus ya sanar da hakan ne a taron da aka yi tsakanin hukumomin kasashen biyu a Abuja.

Ya ce yana farin cikin jaddada yarjejeniyar da ke tsakaninsu don ci gaba da tabbatar da nasarar jami'an tsaron hadin guiwa.

Ya ce kirkirar MNJTF da kasashen suka yi ya kawo babbar nasara wajen yaki da ta'addanci.

Ya ce akwai bukatar su jaddada yarjejeniyar.

Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi
Boko Haram: An sake jaddada wata yarjejeniya tsakanin Najeriya da Chadi
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: Gwamnatin Chadi ta yi martani mai zafi a kan zargin da ake mata

"Akwai bukatar mu nemi sabbin hanyoyin kawo karshen Boko Haram kuma wannan taron zai samar da amintattaun hanyoyin fatattakar ta'addancin.

"Muna bukatar sabbin tsare-tsare wajen kawo karshen ta'addanci in har muna son yankunanmu su zauna lafiya," yace.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, mayakan Boko Haram din sun addabi yankin Arewa maso gabas din ne tun 2009.

Daga bisani ne suka tsallaka kasashen Nijar, Chadi da Kamaru, wanda ya jawo gaggawar daukar mataki.

Ministan ya ce duk da nasarorin da aka samu wajen yakar ta'addancin, Najeriya ta matukar damuwa da yadda 'yan ta'addan ke ci gaba da kaiwa dakarunta hari.

Ya kara da nuna alhinin yadda garkuwa da mutane, dabanci da sauran miyagun ayyuka suka yawaita a kasar nan.

Ya kara da cewa, rundunar sojin kasar nan, ba su sassauta ba wajen kokarin yakar duk wata kungiyar ta'addanci da ke yankin.

Magashi ya ce babban kalubalen da duniya ke fuskanta a yanzu shine annobar coronavirus.

Ministan tsaro na kasar Chadi, Mahamat Aba-Ali Soilah ya yi alkawarin bada goyon baya a kan wannan lamarin.

Ya kara da cewa gwamnatin Chadi za ta rike wannan yarjejeniyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel