Duk da mutuwar mutum daya sakamakon Coronavirus, gwamnatin Katsina ta janye dokar hana Sallar Juma'a

Duk da mutuwar mutum daya sakamakon Coronavirus, gwamnatin Katsina ta janye dokar hana Sallar Juma'a

Gwamnatin jihar Katsina ta janye dokar dakatad da Sallar Juma'a a jihar bayan ganawar shugabannin addini, sarakunan gargajiya da jami'an tsaro a jhar.

Hakan ya biyo bayan mutuwar wani Likita mazaunin garin Daura, Dakta Aliyu Yakubu, sakamakon cutar a makon nan.

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, a jawabin da ya saki ranar Laraba ya ce an janye dokar dakatad da Sallolin Juma'a amma akwai sharruda da aka kindaya na kiwon lafiya da tsaro.

A cewarsa, an shawarci Limaman Juma'a su takaita hudubobinsu domin sallamar Masallatai cikin kankanin lokaci.

“Muna baiwa mutane shawara su rika baiwa juna tazara tare da bin dukkan dokokin da aka kindaya.“

Duk da mutuwar mutum daya makamakon Coronavirus, gwamnatin Katsina ta janye dokar hana Sallar Juma'a
Duk da mutuwar mutum daya makamakon Coronavirus, gwamnatin Katsina ta janye dokar hana Sallar Juma'a
Asali: Facebook

KU KARANTA Gwamnatin Bauchi zata rage albashin ma'aikatan jihar don yakar Coronavirus

Idan baku manta ba, a ranar 28 ga Maris, Daruruwan matasa ne suka ci karo da 'yan sanda a karamar hukumar Kusada da ke jihar Katsina a kan damke wani limamin garin da aka yi.

'Yan sandan sun kama limamin sakamakon karantsaye da yayi ga dokar gwamnatin jihar da ta hana kowanne taron addinin a matsayin hanyar hana yaduwar muguwar cutar coronavirus.

Majiya mai karfi ta bayyana cewa wasu 'yan sandan sun ziyarci gidan malamin ne mai suna Malam Hassan.

Sun bukaci tafiya da shi don amsa tambayoyi a kan dalilin da yasa ya yi jam'in, lamarin da mazauna yankin basu so ba.

Abinda 'yan sandan suka yi kuwa ya matukar fusata matasan, wanda yasa har suka bi su ofishinsu a Kusada.

Bayan yunkurin kwace Malam daga hannun 'yan sandan ya gagara, sai suka bankawa ofishin 'yan sandan wuta har hakan ya jawo mutuwar dan sanda daya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel