Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 10, Jimilla 184

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 10, Jimilla 184

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane goma da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Alhamis inda tace: “An tabbatar da mutane goma sun kamu da #COVID19 a Najerya. 3 a Abuja, 7 a Legas, .“

“Dai-dai Karfe 8:00 na daren 2 ga Afrilu, mutane 174 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami ashirin, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“

Ga jerin jiha-jiha:

Lagos- 98

FCT- 38

Osun- 14

Oyo- 8

Akwa Ibom- 5

Ogun- 4

Edo- 4

Kaduna- 4

Bauchi- 3

Enugu- 2

Ekiti- 2

Rivers-1

Benue- 1

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An sallami mutane 11 daga asibiti a Legas bayan sun warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 10, Jimilla 184
Coronavirus 10, Jimilla 184
Asali: UGC

Gwamnatin jihar Legas ta alanta sallamar masu fama da cutar Coronavirus 11 daga asibitinta dake unguwar Yaba.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis, 2 ga Afrilu, 2020. A cewar Sanwo-Olu, marasa lafiya maza tara ne da mata biyu.

Yace: "Ina farin cikin bayyana muku, al'ummar jihar Legas cewa mun sallami marasa lafiya 11 daga asibitinmu dake Yaba."

"Sun samu isasshen lafiya, sun warke kuma gwaji ya nuna cewa sun tsira daga cutar COVID19 kuma tuni tun tafi gidajensu."

"Marasa lafiyan sun hada da maza tara da mata biyu. Sakamakon gwaji biyu da aka gudanar ya nuna cewa basu dauke da cutar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel