Annobar Corona: Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya kyautar Yuro miliyan 5.5

Annobar Corona: Gwamnatin kasar Jamus ta baiwa Najeriya kyautar Yuro miliyan 5.5

Gwamnatin kasar Jamus ta dauki alwashin baiwa Najeriya tallafin makudan Yuro miliyan 5.5, kimanin naira biliyan 2.2 kenan a matsayin tallafinta sakamakon bullar annobar Coronavirus a kasar.

Punch ta ruwaito ofishin kula da walwalar jama’a a Najeriya ce ta tabbatar da haka, inda tace ofishin jakadancin Jamus a Najeriya ce ta yi wannan alkawari, a daidai lokacin da kasashen nahiyar Afirka ke fama da annobar.

KU KARANTA: Na dauki babban darasi daga kamuwa da Coronavirus – Babandede, shugaban Immigration

Ofishin kula da walwalar jama’an ta sanar da taimakon ne a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda ta ce tallafin zai taimaka wajen kulawa da talakawa marasa karfi da abinci, ruwan sha da kuma matsuguni.

A wani labarin kuma, hukuma ta sako wani mazaunin garin Zaria na jahar Kaduna da ya dawo daga jahar Legas a ranar Juma’a, amma aka killace shi a babban asibitin Gambo Sawaba sakamakon zargin da ake yi na cewa yana dauke da kwayar cutar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito hukumar asibitin ta sallami mutumin ne bayan samun sakamakon gwajin da hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta yi masa, wanda ya nuna tabbas mutumin ba ya dauke da cutar.

Mutumin mai suna Iliyasu Mukhtar ya koma Zaria ne daga jahar Legas, sai dai koda ya isa gida sai suka same shi yana fama da zazzabi, kuma baya iya numfashi yadda ya kamata, nan da nan aka garzaya da shi Gambo Sawaba don samun kulawa, inda a can aka killace shi don gudanar da bincike.

A hannu guda kuma, shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede ya bayyana cewa kamuwa da yayi da cutar Coronavirus ta sa ya zamto mutum mai tawali’u, tare da kaskantara da kan sa.

Babandede ya bayyana haka ne daga inda aka killace shi a karo ba farko, inda yace sakamakon gwajin da aka masa ne ya nuna yana dauke da cutar bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya a ranar 22 ga watan Maris.

Babandede ya nemi yan Najeriya su cigaba da addu’ar Allah Ya kiyaye yaduwar cutar, domin kuwa idan hakan ya faru zata kwashi rayukan jama’a da dama, kwanturolan ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo, inda yace jama’an kauyensu da sauran yan Najeriya suna ta masa addua’r samun sauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel