Ku kyale asibitoci masu zaman kansu su gudanar da gwajin Coronavirus – Dangote ga FG

Ku kyale asibitoci masu zaman kansu su gudanar da gwajin Coronavirus – Dangote ga FG

Fitaccen attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya shawarci gwamnatin tarayya a kan ta baiwa asibitoci da cibiyoyin gwaje gwaje masu zaman kansu daman fara gudanar da gwajin annobar cutar nan mai toshe numfashi, watau Coronavirus.

A cewar Dangote, idan gwamnati ta bayar da wannan dama, hakan zai rage tsawon lokacin da aka dauka kafin fitowar sakamakon gwajin cutar, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shi.

KU KARANTA: Gwamnan jahar Ondo ya killace kansa bayan mu’amala da gwamnan Bauchi

Dangote ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 25 ga watan Maris a jahar Legas inda yace: “A yanzu cibiyoyin gwaje gwaje guda biyar ne kacal na gwamnati dake gudanar da gwaje gwaje a duk fadin Najeriya, duk kuwa da cewa muna da cibiyoyi masu kyau da ka iya gudanar da wannan gwaji, amma basu samu amincewar gwamnati ba.”

Haka zalika Dangote ya bayyana kokarin da kamfanoni masu zaman kansu a karkashin jagorancinsa da babban manajan bankin Access Bank, Herbert Wigwe, suke yi game da yaki da cutar Coronavirus.

“Muna aiki tare da gwamnatin jahar Legas domin samar da tantuna masu dauke da kayan aiki na zamani inda za’a dinga killace masu dauke da cutar, tare da gudanar da gwaji, da kuma kulawa dasu.

“Muna kara samar da cibiyar Coronavirus guda daya a Victoria Island Legas, za kuma mu dauko hayar kwararru daga sassan duniya domin taimaka ma jami’an kiwon lafiyarmu tare da horas da su.

“COVID-19 ta shafemu duka, kuma tana barazana ga kiwon lafiyarmu, tattalin arzikinmu, zamantakewarmu da kuma walwalarmu, don haka akwai bukatar hada kai domin yakar wannan makiyinmu.” Inji shi.

Daga karshe Dangote ya bayyana cewa za su gudanar da ayyukan cikin lokaci domin samun biyan bukata. Sauran kamfanonin dake cikin wannan hadaka sun hada da Zenith Bank, Guaranty Trust Banka, MTN, ITB da sauransu.

A wani labarin kuma, karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Aliyu ta bayyana cewa ta hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta gudanar da gwajin annobar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus a kanta.

Ramatu ta bayyana cewa ta yi mu’amala da mutanen da gwaji ya tabbatar da cewa suna dauke da cutar, hakan ne yasa wajibi ita ma ta yi wannan gwaji domin sanin matsayinta.

Zuwa yanzu dai hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta bayyana cewa daga cikin mutane 46 da aka samu suna dauke da cutar Corona, mutane 8 a babban birnin tarayya Abuja su ke, daga cikinsu har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abb Kyari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel