COVID-19: Yadda Bill Gates yayi hasashen annobar a 2015 da 2018 (Bidiyo)

COVID-19: Yadda Bill Gates yayi hasashen annobar a 2015 da 2018 (Bidiyo)

- A shekaru biyar da kuma biyu da suka gabata, hamshakin mai kudin duniya, Bill Gates yayi hasashen wannan muguwar annobar ta duniya

- Gates ya sanar da hakan ne a yayin tsokaci a jawabin da aka yi na Massachusetts Medical Society a Boston a watan Afirilu na 2018

- A yayin da yake tsokaci a kan kokarin masu bincike a kan magungunan HIV, zazzabin cizon sauro da Polio, babban mai kudin yayi hasashen irin abinda ke tunkaro duniya

Kasa da shekaru kafin barkewar mugunyar cutar coronavirus da ta lashe rayukan jama'a a duniya, babban hamshakin mai kudi Bill Gates ya ja kunnen duniya a kan a dage da tarbar mummunan kalubalen cuta a fadin duniya.

Gates ya sanar da hakan ne a yayin tsokaci a jawabin da aka yi na Massachusetts Medical Society a Boston a watan Afirilu na 2018.

A yayin da yake tsokaci a kan kokarin masu bincike a kan magungunan HIV, zazzabin cizon sauro da Polio, babban mai kudin yayi hasashen irin abinda ke tunkaro duniya.

"Akwai wani bangare daya da duniya bata samun ci gaba, shine shirya tarar annoba," Gates yace.

"Ya kamata wannan ya zama abinda ya damemu gaba daya, saboda idan tarihi ya koya mana darasi, zamu gane cewa za a iya samun barkewar annoba a duniya." ya kara da cewa.

COVID-19: Yadda Bill Gates yayi hasashen annobar a 2015 da 2018 (Bidiyo)
COVID-19: Yadda Bill Gates yayi hasashen annobar a 2015 da 2018 (Bidiyo)
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Babbar magana: An nade kafet din Masallacin Harami a Saudiyya saboda coronavirus

Ya shawarci cewa a habaka wasu bangarori. "Abinda duniya ke bukata sannan muke bukata don kariya a garemu shine makamai da kuma hanyar shawo kan annoba da gaggawa," Gates yace.

Mashahurin mai arzikin ya kara da cewa idan annobar 1918 ta sake dawowa a yau, kusan mutane miliyan 33 na duniya ne zasu mutu a cikin watanni shida kacal.

Kamar yadda yace, gidauniyarsa na kokarin habaka wani riga-kafi na kowacce irin cuta a duniya.

"Amma kuma ba dole bane annobar nan gaba kadan ta zama masassara,'" Gates yace.

"Babu shakka, zata zamo wata kwayar cuta ce da zamu gani a karo na farko. Ina matukar goyon bayan habaka riga-kafi, amma ba dole bane su zama makama ba idan annoba ta barke," Gates yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel