An haifeni babu mahaifa kuma koda daya gareni - Julian Peter

An haifeni babu mahaifa kuma koda daya gareni - Julian Peter

- An haifa Julian Peter ne babu mahaifa kuma da koda daya, amma hakan bai cire mata walwalar rayuwarta ba

- Budurwar mai shekaru 29 ta gano halin da take ciki ne a lokacin da take da shekaru 17 a duniya

- Julian ta ce ta karba halin da take da hannu bibbiyu kuma ana kiran shi ne da Mayer-Rokitansky-Kuster-Hauser a likitance

Julian Peter budurwa ce mai shekaru 29 'yar asalin kasar Kenya wacce aka haifa babu mahaifa kuma da koda daya a jikinta. Ta bayyana labarinta wanda ake samun shi a cikin mata 5,000.

An haifa Julian ne da ciwon Mayer-Rokitansky-Kuster-Hauser (MRKH) a likitance kuma ta gano hakan ne a lokacin da take da shekaru 17 a duniya kuma tana makarantar sakandare.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, Julian ta yi kwanaki uku tana kuka bayan ta gano matsalar da ke tare da ita.

Legit.ng ta gano cewa budurwar ta hadu da mutane masu tarin yawa a kasar Kenya masu irin matsalarta. Don haka ne ta rungumi kaddararta da gaggawa.

Julian ta ce: "Bani da mahaifa don haka ban taba yin jinin al'ada ba. Wannan na saba dashi, don haka bana damuwa."

Julian ta ce: "Wani ya bani shawarar in je wani waje ayi min addu'a. Wani mutum kuwa ya ce saboda daga Ukambani nazo, akwai yuwuwar kakata ce mayya."

An haifeni babu mahaifa kuma koda daya gareni - Juliana Peter

An haifeni babu mahaifa kuma koda daya gareni - Juliana Peter
Source: Twitter

KU KARANTA: Yadda muke sayar da 'yan Najeriya a matsayin bayi a kasar Libya

An bude wa Julian bular gabanta ne a 2018, ma'ana za ta iya saduwa amma sai tace bata shirya ba a yanzu.

Ta kara da cewa: "Ban shirya aure ba amma idan ina so zan dauko yara daga gidan marayu."

A wani labari na daban, Darius Simmons na daya daga cikin mutanen da ba su bari nakasa ta hana su nasara a rayuwarsu ba.

Simmons na da yatsu uku a hannunshi na dama da kuma yatsa daya a hannun shi na hagu. Da kanshi ya koya wa kanshi kida da Piano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel