Budurwa dauke da tsohon ciki ta sha guba bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure

Budurwa dauke da tsohon ciki ta sha guba bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure

A ranar Alhamis dinnan ne wata budurwa mai shekaru 20 daga jihar Anambra tayi kokarin kashe kanta bayan ta gano cewa saurayinta yana da aure

Budurwar ana zargin ta sha guba ne domin ta kashe kanta kowa ma ya huta.

Budurwar da aka bayyana sunanta da Oluchi daga garin Obosi dake cikin karamar hukumar Idemili cikin jihar ta Anambra.

Rahotanni sun bayyana cewa an ceto rayuwarta sannan kuma 'yan sanda suka kama ta da zargin kokarin kashe kanta.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce: "A ranar 19 ga watan 3 shekarar 2020 da misalin karfe 4 na yamma, an kai rahoto ofishin 'yan sanda na Awada cewa wata budurwa mai karancin shekaru da aka bayyana sunanta da Oluchi Akabilo ta sha guba da niyyar kashe kanta.

"Budurwar ana zargin tana da ciki da saurayin nata mai suna Chinedu wanda ba a san ainahin sunan mahaifinsa ba, an bayyana cewa yana da aure har da 'ya'ya.

"Hankalinta yayi matukar tashi bayan ta gano cewa yana da aure, inda taje ta sayo guba da kudin da saurayin ya bata naira dubu goma domin ta zubar da cikin da ta dauka.

"An garzaya da ita asibiti mafi kusa dake garin Onitsha, inda 'yan sanda suka kai ta kuma likitoci suka yi iya bakin kokarinsu domin su ceto rayuwarta.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar ya kara da cewa: "Yanzu haka muna cigaba da gabatar da bincike akan lamarin, kuma mun sanya jami'anmu su nemo duk inda saurayin ya shiga, domin tabbatar da ainahin abinda ya faru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel