Babu wanda cutar Coronavirus ta kama a cikin yan bautan kasa - NYSC

Babu wanda cutar Coronavirus ta kama a cikin yan bautan kasa - NYSC

Hukumar NYSC ta musanta rade radin da ake yayatawa ne cewa wai akwai wani dan bautan kasa daya kamu da cutar Coronavirus, inda ta ce babu gaskiya a cikin rade raden.

A ranar Laraba ne NYSC ta sanar da garkame dukkanin sansanonin horas da matasa masu yi ma kasa hidima dake fadin Najeriya tare da sallamar matasan daga sansanin.

KU KARANTA: Nan bada jimawa ba za mu fara daukan sabbin Yansanda 10,000 – Minista

Jaridar Punch ta ruwaito hukumar NYSC ta bayyana haka ne bayan wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da suka gudanar a ranar Laraba, inda suka ce sun yanke shawarar kulle sansanonin horon yan bautan kasar ne saboda gudun yaduwar cutar Coronavirus.

Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare ya bayyana cewa: “A yau mun kulle sansanonin horas da yan bautan kasa a duk fadin Najeriya, za mu biya yan bautan kasan, kuma an turasu wuraren da za su yi aiki. Mun yi wannan ne don hana yaduwar cutar Coronavirus.

“Amma za mu dawo da matasan bautan kasa zuwa sansanin domin a cigaba da horas dasu da zarar an samu saukin cutar, kamar yadda aka yi a shekarun baya lokacin da cutar Ebola ta bayyana. Don haka muna sanar da cewa babu dan bautan kasan daya kamu da cutar. Kuma babu wani jami’in hukumar da ya kamu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da bullar annobar cutar Coronavirus, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar muhawara a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ta nemi gwamnatin Najeriya ta dauki kwararn matakai domin kare yaduwar cutar a Najeriya.

“Majalisa ta yi kira ga shugaban kasa ya fito ya yi ma yan Najeriya bayani game da wannan matsalar, manyan kasashen duniya sun yi haka, idan ya fito yayi jawabi ga yan Najeriya, sai an fi daukan maganan da muhimmanci.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel