Mawaki Wizkid ya yi zazzafan martani ga majalisar kasar nan a kan haramta shigo da janareto
- Mawaki Wizkid ya yi martani ga majalisar dattijai a kan dokar haramta amfani da janareto
- Mawakin ya bayyana hakan ne a wata wallafar da yayi inda ya bukaci a saki wuta ta sa’o’i 24 kafin haramta amfani da janareton
- Wannan martanin na Wizkid ya jawo cece-kuce daga masu bibiyar shafin shi na twitter
Mawaki Ayodeji balogun wanda aka fi san da Wizkid ya yi magana a kan kokarin haramta shigo da janareto kasar nan don samar da wutar lantarki da majalisar dattijai ke yunkurin yi.
Kamar yadda mawakin ya bayyana a shafin shi, ya kushe wannan yunkurin na garkame mutane a gidajen yarin kasar nan matukar suka shigo da janareton.
Kamar yadda mawakin ya wallafa, bai dace a fara wannan yunkurin ba ba tare da an samarwa kasar nan wuta ta sa’o’i 24 ba a kowacce rana.
KU KARANTA: Bayan korata a wajen aiki iyalina ta gudu, yanzu kuma tana so ta dawo bayan taji na sami miliyan 15 - Wani na neman shawara
Majalisar dattijan kasar nan ta fara yunkurin saka dokar daure duk wanda ke siya da siyar da injin samar da wutar lantarki na shekaru 10. Dokar na son hana shigowa da kuma amfani da janareto a kasar nan tare da shawo kan gurbacewar iska.
Dokar haramta amfani da janareton an karanta ta karo na farko ne a zaman majalisa a ranar Laraba. Mataimakin shugaban kwamitin noma da raya karkara, Sanata Muhammed Enagi Bima na jam’iyyar APC ne ya dau nauyin dokar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng