Coronavirus: Ku daina musafaha, ku daina runguma - Minista ya gargadi yan Najeriya

Coronavirus: Ku daina musafaha, ku daina runguma - Minista ya gargadi yan Najeriya

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya gargadi yan Najeriya su rage halin musafaha da runguman juna domin takaita yaduwar annobar Coronavirus da ta addabi duniya.

Ministan ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da fara wani gini a unguwar Karshi dake Abuja ranar Alhamis.

Ministan ta yayi kira ga yan Najeriya su rika nesa-nesa da juna kuma su guji wuraren da akwai cincirindon mutane.

Yace “Ku daina musafaha da juna, ku daina rungumar juna illa yan uwanku na jini. Ku rika nesa-nesa akalla kafa uku da mutum.“

Ministan ya shawarci yan Najeriya su rika gaisawa ta hanyar durkusa da daura hannu a kirji.

Aregbesola ya kara da cewa annobar Coronavirus ta zama babbar annoba ga duniya kuma idan ba a dau mataki ba za ta zama mana babbar kalubale.

“Wajibi ne mu kiyayi Coronavirus kuma mu mayar da hankali wajen kawar da ita. Wannan wajibi ne a kanmu da iyalanmu da alummarmu.“ A cewarsa

A bangare guda, Ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Enahire, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a sallami dan kasar Italiyan da ya kawo Coronavirus Najeriya.

TVC News ta ruwaito cewa Ministan lafiyan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja yayinda yake tattaunawa da jami'ai daga kasashen waje kan matakan da gwamnatin tarayya ke dauka wajen dakile yaduwar cutar.

Ministan ya jaddada cewa har yanzu mutane biyu kadai ke dauke da cutar a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel