Zan iya hada mijina da karuwa, na san zai iya gundura da ni kadai - Budurwa

Zan iya hada mijina da karuwa, na san zai iya gundura da ni kadai - Budurwa

- Wata budurwar Najeriya tayi ikirarin cewa ba ta damu ba idan mijinta na neman mata barkatai

- Kamar yadda Funke Fatai ta bayyana, da kanta za ta samowa mijinta wasu karuwan don ya ji dadin rayuwar shi ta duniya

- Wannan wallafar kuwa ta jawo mata caccaka daga bakin mata masu miji da kuma wadanda basu da mijin

Wata budurwar Najeriya tayi ikirarin cewa ba ta damu ba idan mijinta na neman mata barkatai. Kamar yadda ta wallafa, babu dadi mutum ya nace cin abu daya a kowacce rana. A kalla da namiji na bukatar abinci kala-kala. Idan kuwa haka gaskiya ne, toh tabbas ba zai so mace daya ba.

Kamar yadda Funke Fatai ta bayyana, da kanta za ta samowa mijinta wasu karuwan don ya ji dadin rayuwar shi ta duniya.

Zan iya hada mijina da karuwa, na san zai iya gundura da ni kadai - Budurwa
Zan iya hada mijina da karuwa, na san zai iya gundura da ni kadai - Budurwa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Soyayya ruwan zuma: Budurwa ta tara N1.8m, ta bawa saurayinta kyauta domin ya sayi mota

“Ina daga cikin matan da ba zasu gallaza wa mijinsu ta hanyar cewa sai ni kadai zai kwanta da ni ba. Ni ko saurayi ne muke tare, na kan hada shi da wata kawata wacce na amince da ita ya kwanta don jin dadin rayuwar shi.

“Shinkafa na da dadi amma akwai wasu lokuta da za ki ba namiji dama ya mori taliya ko tuwo.” Ta ce.

Wannan wallafar kuwa ta jawo mata caccaka daga bakin mata masu miji da kuma wadanda basu da mijin. Wasu na ganin cewa don dai ba aure tayi bane kuma ba ta san ciwon zama da miji ba balle ta amince mishi da bin karuwai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel