Lakcarorin jami’an da suka ku yin rijista a manhajar IPPIS ba zasu samu albashin Febrairu ba – Ministar Kudi

Lakcarorin jami’an da suka ku yin rijista a manhajar IPPIS ba zasu samu albashin Febrairu ba – Ministar Kudi

Ministar kudi da kasafin kudi ta ce duk lakcaran da bai yi rijista a manhajar biyan albashin bai daya na IPPIS ba zai samu albashin watan Febrairu da ya kare ba.

Yayinda take magana da manema labarai a Kano ranar Alhamis, ministar tace kashi 55 cikin 100 na mambobin kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU sun yi rijista a manhajar.

A watan Junairu, gwamnatin tarayya ta bada umurnin daina biyan lakcarori da dukkan ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandaren da ke Najeriya da suka ki rijista a manhajar IPPIS.

Lakcarorin jami’an da suka ku yin rijista a manhajar IPPIS ba zasu samu albashin Febrairu ba – Ministar Kudi

Ministar Kudi
Source: UGC

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta lashi takobin tafiya yajin aiki idan basu samu albashinsu ba.

ASUU ta yi watsi da dukkan umurnin da gwamnatin tarayya ta yiwa ma’aikata na rijista saboda hakan zai rage musu karfi.

Amma, Zainab ta ce duk da cewa akwai taurin kai ta bangaren ASUU, manufar manhajar ita ce rage rashawa.

Tace: “Abin takaici shine duk wani matakin gyaran da ka dauka sai ka fuskanci yan tawaye. Mun fuskanci kalubale daga ASUU kan aiwatar da IPPIS kuma ina farin cikin fada muku cewa akalla kasha 55% na mambobin ASUU sun yi rijista.”

“Wadanda kuma basu yi rijista ba, ba zasu samu albashin Febrairu ba.”

“Na san yanzu mun samu ma’aikatan bogi 70,000 da muka gano a shirin kuma muna sa ran zamu kawar da su gaba daya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel