Rikicin cikin gida: Sabon shugaban ISWAP ya halaka manyan kwamandoji 5

Rikicin cikin gida: Sabon shugaban ISWAP ya halaka manyan kwamandoji 5

Sabon shugaban kungiyar Boko Haram tawariyya, watau ISWAP dake da alaka da kungiyar yan ta’adda ta duniya, ISIS, Lawan Abubalar wanda ake ma lakabi da Ba Lawan ya fara kokarin tabbatar da karfin ikonsa ta hanyar kashe manyan yan majalisar koli ta ISWAP guda 5.

Premium Times ta ruwaito daga cikin wadanda Ba Lawan ya kashe har da tsohon shugaban ISWAP, Abu Abdullahi Umar Al Barnawi, inkiya Ba Idrissa, kamar yadda majiyoyi suka bayyana mata a ranar Lahadi a garin Diffa da Maiduguri.

KU KARANTA: Bahallatsar kwangilar sayo makamai: Rabiu Kwankwaso ya wanke Abba da Ganduje

Rikicin cikin gida: Sabon shugaban ISWAP ya halaka manyan kwamandoji 5

Kungiyar Boko Haram
Source: Facebook

“Wannan shi ne kisan gilla mafi muni da aka taba samu a cikin kugiyar inda aka kashe shugaban kungiyar a zuwa daya.” Kamar yadda binciken majiyarmu tare da hadin gwiwar HumAngle Media Foundation ya tabbatar, wanda ya yi hasashen Ba Lawan zai kasance mara Imani.

Bayan kifar da gwamnatin Ba Idrisa a watan Feburairu ne, sai Ba Lawan ya kama shi tare da Mohammad Bashir, Mustapha Jere, Ali Abdullahi, da kuma Baba Mayinta, sa’annan ya tsare su duka, wnada hakan ya janyo bore daga bangaren mabiya Ba Idrisa a ranakun 26 da 27 ga watan Feburairu.

“Mabiyan shuwagabannin ISWAP da aka kashe sun yi kokarin kwatosu da karfin tuwo, inda suka kaddamar da hare hare a sansanin ISWAP har suka cikin sashin da suke bauta da nudin kwatosu, hakan ya sabbaba musayar wuta tsakanin bangarorin biyu a ranar Alhamis 27 ga watan Feburairu.

“A nan aka harbi Abu Mus’ab, dan shugaban Boko Haram Muhammad Yusuf, wanda babu tabbacin mutuwarsa ko kuma ya sha, yayin da Mustapha Krimana ya tsallake rijiya da baya.” Inji rahoton.

Wannan hargitsi ya sa lallai Ba Lawan ya lashi takobin kashe Ba Idrissa da sauran kwamandojin ISWAP hudu, inda ya shaida ma mabiyansu cewa tsofaffin shuwagabannin na kokarin tserewa zuwa kasar kafirci ne domin su jagoranci wata sabuwar da za ta yakesu, don haka ya kashe su.

Masana ayyukan Boko Haram na ganin babban laifin Ba Idrisa shi ne yana da saukin ra’ayi, saboda an san shi da kau da kai ga mutanen dake adawa da ISWAP, ko kuma mutanen da ake zargi suna ma gwamnati leken asiri a cikin ISWAP.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel