Majalisa ta haramta ma Buhari kashe kudaden Abacha a titin Abuja zuwa Kano

Majalisa ta haramta ma Buhari kashe kudaden Abacha a titin Abuja zuwa Kano

Kwamitin majalisar dokoki mai kula da ayyuka za ta gayyaci ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola da sauran manyan jami’an ma’aikatar domin su gurfana a gabanta game da shirin gwamnati na kashe kudaden Abacha a dala miliyan 308 a ayyukan gine ginen tituna.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito majalisar ta yanke shawarar gayyatar ministan da jami’an ne a wani bincike da ta kaddamar biyo bayan shawarar da majalisar wakilai ta yanke kan bukatar a bincike a aikin titunan Legas zuwa Ibadan, Abuja-Kaduna-Zaria-Kano da gadar yankin Neja.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus

Kwamitin a karkashin Injiniya Abubakar Kabir Abubakar ta fadada bincikenta har zuwa kan yadda gwamnatin tarayya ta yi nufin kashe makudan kudaden da ta amso daga kasashen waje mallakin tsohon shugaban kasa Janar Abacha.

“An bamu daman gudanar da bincike, za mu gayyaci minista, kamfanin Berger da saura masu ruwa da tsaki, a ranar Litinin za mu tura musu wasikar gayyata tare da ranar da muke bukata su bayyana a gabanmu.

“Baya ga tafiyar hawainiyar da aikin titunan yake, bai kamata a kashe dala miliyan 308 a aikin titunan ba bayan an ware kudaden da za’a kashe musu tun farko, kimanin watanni 2 da suka kamata muka gayyaci Julius berger muka nuna musu bacin ranmu game da aikin da suka yi duba da kudin da aka basu.” Inji shi.

Idan za’a tuna ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta bayyana cewa za ta kashe kudaden Abacha a gina hanyoyin Legas-Ibadan, Abuja – Kano, da aikin gina gadar Neja ta biyu.

A wani labarin kuma, wata mata dattijuwa mai shekaru 70 a duniya, wanda aka sakaya sunanta, ta jagoranci matasa mafarauta zuwa cikin dazuka inda suka kashe yan bindiga 40 a jahar Neja.

Guda daga cikin mafarautan dake cikin tawagar wannan jaruma, Mallam Alhassan ya bayyana cewa ta jagorance su zuwa cikin dajin Zuguruma a karamar hukumar Mashegu na jahar, inda a can suka yi artabu da yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel