Yanzu-yanzu: Mutum 13 sun rasu sakamakon hatsarin mota a hanyar Bauchi zuwa Jos

Yanzu-yanzu: Mutum 13 sun rasu sakamakon hatsarin mota a hanyar Bauchi zuwa Jos

A kalla mutane 13 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota da suka faru a jihar Bauchi a daren ranar Alhamis da safiyar ranar Juma'a.

The Punch ta ruwaito cewa hatsarin motocin sun faru ne a Tashan Maiturare da Takandan Giwa duk a babban titin Bauchi zuwa Jos a karamar hukumar Toro a jihar ta Bauchi.

A hatsarin na farko wadda ya faru misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis, a kalla mutane 11 ne suka mutu nan take yayin da wasu da dama suka jikkata.

Yanzu-yanzu: Mutum 13 sun rasu sakamakon hatsarin mota a hanyar Bauchi zuwa Jos
Yanzu-yanzu: Mutum 13 sun rasu sakamakon hatsarin mota a hanyar Bauchi zuwa Jos
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hargitsi tsakanin shugabannin Boko Haram da ISWAP: Akwai yuwuwar Shekau ya sheka lahira

Hatsarin na biyu ya faru ne a subahin ranar Juma'a kusa da kauyen Takandan Giwa yayinda wata mota ta kauce daga titi ta fada cikin daji inda mutane biyu suka mutu yayin da wasu kuma suka samu rauni.

Da aka tuntube shi, Shugaban sashin ayyuka na hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi, Ibrahim Abubakar ya tabbatar da afkuwar hadduran amma ya ce har yanzu suna tattara bayanai.

A wani rahoton, mun kawo muku cewa dakarun sojojin Najeriya sun kama wata da ake zargin 'yan bindiga ce, Zainab Abubakar, a Unguwan Salaha, Mararaban Jos a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Rundunar sojin ta ce a ranar Alhamis cewa binciken da aka fara gudanarwa a wayar salular wace ake zargi 'ya nuna ta tana tika rawa rataye da bindiga AK - 47 a wuyan ta.'

The Punch ta ruwaito cewa Dakarun sojojin 1 Division Garrison a karkashin Operation Mesa ta kama Zainab Abubakar ne a ranar Litini.

Mai kula da sashin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Kwanel Aminu Iliyasu, ya tabbatar wa manema labarai kama wacce ake zargin inda ya ce Dakarun 1 Division Garrison ta kama wata 'yar bindiga mace a Unguwan Salaha a Mararaban Jos.

Binciken da aka gudananar da fari ya nuna bidiyo a cikin wayar ta tana tika rawa da bindiga AK-47 a wuyan ta wurin wani taron Party.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel