Da duminsa: An kulle kamfanin Siminti a Ogun kan tsoron Coronavirus

Da duminsa: An kulle kamfanin Siminti a Ogun kan tsoron Coronavirus

Gwamnatin jihar Ogun ta sanar da cewa an kulle kamfanin Simintin Larfarge dake Ewekoro a jihar bayan tabbatar da shigar mutumin da ya kwaso Coronavirus Najeriya harabar kamfanin.

Gwamnatin jihar ta ce, dan kasar Italiyan, wanda yake aiki da kamfanin Larfarge Africa ya ziyarci kamfanin Simintin ranar Talata.

Kwamishnar kiwon lafiyan jihar, Dakta Tomi Coker, wacce ta bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da manema labarai a Abekuta, babbar birnin jihar, ta ce ya fara zazzabi ne kuma aka fara jinyarsa a asibitin dake cikin kamfanin Lafarge kafin komawarsa Legas ranar Laraba.

Kwamishanar, tare da kakakin gwamnan jihar, Remmy Hazzan, da manyan ma'aikatan ma'aikatar sunce masana kwayoyin cuta sun fara tattara dukkan wadanda ya hadu da su a lokacin da je jihar.

Kwamishanar ta ce mutumin ya hadu mutane uku kafin zuwansa jihar Ogun ranar Talata.

Tace: "A awanni 12 da suka gabata, an gano bullar cutar COVID – 19 (Coronavirus) a Najeriya kuma mutumin da ke dauke da cutar ya ziyarci jihar Ogun."

"Mutumin dan kasar Italiya ne, ma'aikaci ne a kamfanin Lafarge dake Ewekoro. Ya zo Najeriya ranar 24 ga Febrairu misalin karfe 9 na dare."

Kafin isarsa jihar Ogun, ya gana da mutane uku, ya kwana a Legas kuma ya zo Ogun da safiyar Talata."

"Ya zauna a dakin otal kuma misalin karfe 4 zuwa 5 na rana, ya fara jin zazzabi da ciwon jiki."

Da duminsa: An kulle kamfanin Siminti a Ogun kan tsoron Coronavirus
Da duminsa: An kulle kamfanin Siminti a Ogun kan tsoron Coronavirus
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria NCDC ta samar da jamian da zasu taimakawa gwamnatin Jihar Legas, waajen dakila bullar coronavirus ta farko a Nigeria.

Darakta Janar na Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria, Dr Chikwe Ihekweazu, ya bayyanawa manema labarai hakan ne a Abuja.

Ihekweazu yace wajibi ne asibitoci su lura sosai su zauna cikin shiri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel