Mun bazama neman duk wadanda ya hadu da su lokacin da ya shigo Najeriya - Gwamnatin Legas kan wanda ya shigo da Coronavirus

Mun bazama neman duk wadanda ya hadu da su lokacin da ya shigo Najeriya - Gwamnatin Legas kan wanda ya shigo da Coronavirus

Gwamnatin jihar Legas ta ce jamianta sun bazama neman dukkan wadanda dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Najeriya ya hadu da su tun ranar da ya shigo.

Kwamishanan kiwon lafiyar jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana hakan inda ya ce an kebance mutumin kuma ana kula da shi.

Yace: “Ku sani cewa duk wanda ya kamu da cutar zai iya fuskantar dan zazzabi kuma ya warke, amma zai iya tsanani a wasu, musamman tsofaffi.“

“Mun kaddamar da ayyukan gaggawa domin kange cutar da hana yaduwa.“

“Muna tabbatarwa dukkan mutan jihar Legas da Najeriya cewa tun lokacin da cutar ta bulla a kasar Sin muke shiryawa. Zamuyi amfani da dukkan dukiyar da muke da shi tare da gwamnatin tarayya wajen dakile lamarin.“

Mun bazama neman duk wadanda ya hadu da su lokacin da ya shigo Najeriya - Gwamnatin Legas kan wanda ya shigo da Coronavirus
Gwamnatin Legas kan wanda ya shigo da Coronavirus
Asali: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya tabbatar da bullar cutar Coronavirus mai kisa a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'ar nan 28 ga watan Fabrairu.

A yadda sanarwar ta nuna, cutar ta shafi wani dan kasar Italiya ne wanda yake aiki a Najeriya, wanda ya dawo daga birnin Milan ya shigo Legas a ranar 25 ga watan Fabrairu.

An tabbatar da cutar a jikinshi, bayan gabatar da gwaje-gwaje a babban asibitin koyarwa na jami'ar Legas, a fannin binciken cututtuka.

Ma'aikatar lafiyan ta tabbatar da cewa, mutumin yana nan yana karbar magani, kuma yana samun sauki a hankali a hankali.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin Najeriya karkashin ma'aikatar lafiya na iya bakin kokarinta wajen daukar mataki akan yaduwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel