Gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa Boko Haram ke kai ma kiristoci hari

Gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa Boko Haram ke kai ma kiristoci hari

Gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilin da yasa kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta karkatar da hare harenta ga mabiya addinin kiristanci a Najeriya, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan watsa labaru da al’adun Najeriya, Alhali Lai Mohammed ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba.

KU KARANTA: Har zuwa yanzu ba’a gano maganin annobar Coronavirus ba - Hukumar WHO

A cewar minista Lai, mayakan ta’addancin Boko Haram suna kai ma kiristoci hari ne domin su kunna rikicin addini a tsakanin mabiya mabanbanta addinai daban daban a Najeriya.

“A yanzu yan ta’adda sun sauya dabarun hare harensu, sun koma kai ma kiristoci hare hare da kauyukan kiristoci domin su tayar da yakin addini, tare da jefa kasar cikin tashin tashina ba don komai ba sai domin su gano yadda bambancin addini ke raba kawunan jama’a.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su samar da gudanar da cikakken nazari game da tsare tsare da dabarun da suke amfani dasu a yaki da ISWAP, don duba yiwuwar kirkiro sabbin dabaru.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito shugaba Buhari ya bayar da wannan umarni ne a yayin taron kara ma juna sani a kan harkar tsaro karo na 10 wanda tsofaffin daliban kwalejin tsaro ta kasa, AANDEC suka shirya a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan tsaro, Bashir Magashi ya bayyana cewa sabbin hare haren ta’addanci da ake samu yana faruwa sakamakon shan kayi da kungiyar ISIS ta yi a duniya, amma ya ce an baiwa hukumomin tsaro daman su shawo kan dukkanin wani nau’I na ta’addanci a kasar.

“Samuwar barbashin ISIS a yankin Afirka ta yamma babbar barazana ce a garemu, shi yasa muke hada kai da sauran kasashen Afirka da kungiyoyin kasa da kasa domin takaita wanzuwar ta’addanci tare da karya lagon yan ta’addan.

“Babu shakka Sojojinmu sun ci galaba a kan Boko Haram, kuma akwai bukatar su sake duba tsare tsaren don samun galaba a kan ISWAP dake kai hare hare a sassan kasar.

"Haka zalika suma masu satar mutane da garkuwa dasu muna gargadinsu su daina, ko kuma su fuskanci fushin hukuma domin kuwa an baiwa hukumomin tsaro izinin bin ta kansu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel