Gwamnatin jahar Kaduna ta kalubalanci hukuncin kotu na sakin yan shia 92

Gwamnatin jahar Kaduna ta kalubalanci hukuncin kotu na sakin yan shia 92

Gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ta dauki walshin kalaubalantar hukuncin kotun da ta saki yan Shia 92 ta hanyar daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.

Wata babbar kotun jahar Kaduna ce ta yanke hukuncin sakin yan shi’an tare da wankesu daga tuhume tuhumen dake rataye a wuyarsa bayan kwashe tsawon shekaru hudu a gidajen yari, bayan gwamnatin jahar ta kasa tabbatar da laifin mutanen, a cewar kotun.

KU KARANTA: An yi artabu tsakanin Yansanda da yan fashi a Abuja, 2 sun bakunci lahira

Cikin wata sanarwa da babban lauyar jahar Kaduna, kuma kwamishinar sharia ta jahar, Aisha Dikko ta fitar, ta bayyana cewa gwamnati ba ta gamsu da hukuncin kotun ba, don haka za ta kalubalanci hukuncin a kotun gaba.

“Ba mu gamsu da hukuncin kotun ba, muna kallon hukuncin a matsayin kuskure a doka, kuma babu wani kwakkwaran dalilin yanke wannan hukunci duba da tarin hujjojin da muka gabatar ma kotu a kan wadanda ake kara” Inji ta.

Gwamnatin Kaduna ta tuhumi yan shi’an ne laifukan da suka shafi tashin hankali, kuma tun 2015 ake tsare da su bayan kama su a Zariya lokacin rikicinsu da sojoji wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan 'yan kungiyar ta IMN mabiya Sheikh Ibrahim el-Zakzaky.

Sai a na ta bangaren, kungiyar yan Shia ta IMN ta bayyana hukuncin kotun a matsayin nasara da tabbatar gaskiya da adalci, wanda kuma suke fatan zai zama sanadin sakin jagoransu.

A wani labarin kuma, jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna sun samu nasarar kama wasu miyagun masu garkuwa da mutane guda uku da suka dade suna fitinar jama’an jahar Kaduna, tare ceto wata budurwa daga hannunsu.

Mai magana da yawun Yansandan yankin, Mohammed Jilge ne ya bayyana haka ga menema labaru a ranar Juma’a, 21 ga watan Feburairu a garin Kaduna, inda yace a ranar Laraba suka samu rahoton an sace wata budurwa yar shekara 22 Hadiza Gambo daga Bungel Ladduga na karamar hukumar Kajuru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel