Da duminsa: Cutar Coronavirus ta bulla a nahiyar Afrika

Da duminsa: Cutar Coronavirus ta bulla a nahiyar Afrika

Bayan makonni kimanin uku da bullar cutar Coronavirus wacce aka sani da COVID-19 a kasar Sin, an samu bullar cutar ta farko a nahiyar Afrika ranar Juma'a a kasar Misra.

A wani jawabi, ministan lafiyan kasar Masar ya bayyana cewa sun sanar da kungiyar kiwon lafiyan duniya WHO kuma suna daukan matakan shawo kan lamarin amma bai bayyana suna da asalin wanda ya kamu da cutar ba.

Kungiyar WHO ta bayyana cewa kawo yanzu, mutane 46,550 suka kamu da cutar a fadin duniya.

Dakta Micheal Ryan, diraktan shirye-shiryen gaggawa na kungiyar ya bayyana hakan ne a jawabin da aka daura a shafin ranar gizon WHO ranar Juma'a.

Kasashen da aka tabbatar da bullar cutar sun hada da Misra, Singapore, Birtaniya, Malaysia, Taiwan, Spain, Vietnam, Jamus, UAE, Faransa da Japan.

Sauran sune Thailand, Canada, Australia, Italy, Rasha , Sweden, Finland, Cambodia, da Amurka.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun hallaka mutane 33 a Katsina

Da duminsa: Cutar Coronavirus ta bulla a nahiyar Afrika
Da duminsa: Cutar Coronavirus ta bulla a nahiyar Afrika
Asali: UGC

A bangare guda, Gwamnatin tarayya tayi alkawarin baiwa duk wani masanin kimiyan Najeriyan da ya samo maganin rigakafin cutar Coronavirus kyautan kudi Milyan N36m.

Ministan Kimiya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya yi wannan alkawari ne a Abuja ranar Alhamis a taron walima da aka shiryawa daya daga cikin manyan diraktocin ma’aikatar, Injiniya A Oyefeso, wanda yayi ritaya.

Onu ya ce akwai bukatar Najeriya ta yi nazarin wuri gabanin sauran kasashen duniya wajen kare kanta da cutar.

Ya ce gwamnatin za ta bada gudunmuwar kudi ga masana kimiyan Najeriya wajen samar da magani ga wasu cututtuka da suka addabi kasar.

Yace “ Muna alkawari ga kowani masanin kimiyya a Najeriya da zai iya samar da rigakafin Coronavirus kudi N36m.“

“Muna da magunan gargajiya da dama a kasar nan, da yiwuwan maganin cutar na gonakinmu.“

“Muna kalubalantar masana kimiyanmu su samo maganin cutar kuma lallai kasar zata karrama su.“

WHO ta bayyana Abuja, Kano, Legas, Cross River, Akwa Ibom, Port Harcourt, Enugu, Delta da Bayelsa matsayin jihohin da ya kamata a shirya matakan tsaro idan cutar Coronavirus ta bulla a Najeriya.

Babbar jami'ar WHO, Dhamari Naidoo, ta bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata a taron horar da yan jarida kan cutar Coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel