An amince wa sojojin saman Amurka sa rawani da hijabi

An amince wa sojojin saman Amurka sa rawani da hijabi

Rundunar Sojojin Saman Amurka ta yi sauyi a tsarin kayan dakarun ta inda ta bawa musulmi da masu addinin Sikhs daman saka hijabi ko rawani tare da khakin su na soji.

A cewar CNN, sabon tsarin na sojin ya bawa musulmi da masu addinin sikh ikon saka rawani, barin gemu, barin suman kai mai tsawo da hijabi "muddin za a tsaftace shi kuma ya dace da tsari irin na mazan jiya."

A baya, Musulmi da masu addinin sikh da ke aikin soja su kan rubuta wasikar izinin neman barin su suyi shiga irin ta addinin su ne daya bayan daya a wasu lokutan.

An amincewa sojojin saman Amurka sa rawani da hijabi
An amincewa sojojin saman Amurka sa rawani da hijabi
Asali: Twitter

A kan amince musu da hakan bayan lokaci mai tsawo a mafi yawancin lokuta.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari ya dakatar da Modibbo-Kawu a matsayin shugaban NBC

A cewar sabon tsarin, zai dauki kwanaki 30 kafin a kammala tabbatar da tsarin ga wadanda ke aiki a Amurka, su kuma kwanaki 60 ga wadanda ke wasu kasashen.

Wannan sabon cigaban na nuna cewa sojojin saman za su samu daman yin addininsu kamar yadda ya dace ba tare da samun tangarda ba yayin aiki.

Wasu kungiyoyin kare masu addinin Sikh da musulmi sun ce wannan sabon sauyin da aka yi babban mataki ne wurin kyautatawa masu addinai daban-daban kuma akwai bukatar rundunar sojin ta cigaba da hakan.

Sanarwar da direktan watsa labarai na cibiyar harkokin addinin musulunci na Amurka, Ibrahim Cooper ya fitar ta ce, "Muna goyon bayan sabbin dokokin nan a matsayin wani yunkuri na rungumar jami'an sojojin sama ba tare da la'akari da addinansu ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel