Zamu bada N36m ga duk wanda ya gano magani Coronavirus - Gwamnatin tarayya

Zamu bada N36m ga duk wanda ya gano magani Coronavirus - Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya tayi alkawarin baiwa duk wani masanin kimiyan Najeriyan da ya samo maganin rigakafin cutar Coronavirus kyautan kudi Milyan N36m.

Ministan Kimiya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya yi wannan alkawari ne a Abuja ranar Alhamis a taron walima da aka shiryawa daya daga cikin manyan diraktocin ma’aikatar, Injiniya A Oyefeso, wanda yayi ritaya.

Onu ya ce akwai bukatar Najeriya ta yi nazarin wuri gabanin sauran kasashen duniya wajen kare kanta da cutar.

Ya ce gwamnatin za ta bada gudunmuwar kudi ga masana kimiyan Najeriya wajen samar da magani ga wasu cututtuka da suka addabi kasar.

Yace “ Muna alkawari ga kowani masanin kimiyya a Najeriya da zai iya samar da rigakafin Coronavirus kudi N36m.“

“Muna da magunan gargajiya da dama a kasar nan, da yiwuwan maganin cutar na gonakinmu.“

“Muna kalubalantar masana kimiyanmu su samo maganin cutar kuma lallai kasar zata karrama su.“

KU KARANTA Bayan yanke hukunci, Kotun koli za ta zauna kan korafin Ihedioha da Lyon ranar Talata

Zamu bada N36m ga duk wanda ya gano magani Coronavirus - Gwamnatin tarayya
Zamu bada N36m ga duk wanda ya gano magani Coronavirus - Gwamnatin tarayya
Asali: Twitter

Mun kawo muku a baya cewa Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Abuja, Kano, Legas, Cross River, Akwa Ibom, Port Harcourt, Enugu, Delta da Bayelsa matsayin jihohin da ya kamata a shirya matakan tsaro idan cutar Coronavirus ta bulla a Najeriya.

Babbar jami'ar WHO, Dhamari Naidoo, ta bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata a taron horar da yan jarida kan cutar Coronavirus.

Tace: "Kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO ta bayyana Najeriya matsayin kasa mai mugun hadarin kamuwa da cutar saboda yawan sufuri tsakanin kasar Sin da Najeriya."

Ta ce WHO na aiki kan karfafa tsaro a iyakokin shiga Najeriya da kuma taimakawa wajen gano zafin jiki da fuskokin masu shigowa.

Dhamari Naidoo ta kara da cewa an sanar da dukkan kamfanonin jiragen sama su yi kyakkyawan lura da masu shigowa Najeriya daga Sin.

Kawo yanzu, kididdigan alkalumma sun tabbatar da cutar Corona Virus ta kashe sama da mutane 1500 a kasar Sin, watau China tun bayan bullatar watanni biyu da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel