Sanata Ndume ya fadi mawuyacin halin da Sojoji suka sanya mayakan Boko Haram

Sanata Ndume ya fadi mawuyacin halin da Sojoji suka sanya mayakan Boko Haram

Shugaban kwamitin majalisar dattawan Najeriya mai kula da rundunar Sojan kasa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa a yanzu dakarun rundunar Sojan kasa suna bin mayakan yan ta’addan Boko Haram har zuwa sansanoninsu domin gamawa dasu.

Punch ta ruwaito Ndume ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja a ranar asabar, inda yace Sojojin sun samu kwarin gwiwa ne biyo bayan umarnin da rundunar Sojan kasa ta bayar na su dinga kaddamar da hare hare a kan yan ta’addan ba sai sun jirasu ba.

KU KARANTA: Hotuna: Musulman kasar Japan sun samar da Masallacin tafi da gidanka

Ndume yace a yan kwanakin da suka gabata ma Sojoji sun mayar da biki a kan wasu yan ta’adda a Kalla dake kusa da Dabua, inda suka yi ma yan ta’addan rakiyar Kura har zuwa sansanoninsu, inda suka lalatasu gaba daya.

“Har zuwa ranar lahadi Sojoji suna bin sawun yan ta’addan duk inda suka shiga, har sai da suka cimmasu a sansaninsu kamar yadda kwamandan Birget ya bayyana min, kuma yace sun karkashesu, kuma sun kwashe makamansu.

“Idan har Sojoji suka cigaba da wannan dabaran yakin, zasu samu galaba a kan yan ta’addan, kuma nan bada jimawa ba zasu kawo karshen yakin da aka dade ana fafatawa. Abinda Sojoji suke yi shi ne cizge bishiyar tun daga saiwarta.

“Don haka nake kira ga rundunar Sojan kasa su dinga amsa kiran mazauna kauyukan dake yankunan cikin gaggawa, sa’annan su kara zage damtse a kokarin da suke yi wajen yaki da yan ta’addan. Irin wannan shi ne abinda suka yi a Askira Uba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Katsina ta sanar da kama wasu babura guda 320 tare da yan Achaba 186 biyo bayan kaddamar da dokar haramta aikin babur a cikin garin Katsina a tsakanin wasu lokutta da gwamnatin jahar ta kirkiro.

Wannan doka dai ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Janairu domin taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka cigaba da ta’azzara a jahar. A yanzu dai gwamnati har ta gurfanar da yan Achaban gaban kotu saboda karya dokar.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka, inda yace suna cigaba da gudanar da bincike a kan kyasa kyasai 134 daya danganci karya dokar haramta achaba a Katsina.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel