Yanzu-yanzu: INEC ta soke jam'iyyun siyasa 75, 16 kawai suka rage
Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta soke jam'iyyun siyasa 74 a Najeriya.
Jam'iyyun da suka rage yanzu 16 ne kacal.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana dalilan da yasa aka soke jam'iyyun. Dalilan sune:
1. Saba dokokin rijistan jam'iyyar siyasa a Najeriya
2. Gaza samun 25% na kuri'u a jiha ko daya a zaben shugaban kasa da ya gabata, sannan gaza smaun 25% na kuri'u a karamar hukuma ko daya a zaben gwamnonin jihohi 36
3. Gaza cin zabe a yanki daya a zaben shugaban karamar hukuma a kananan hukumomi 774, gaza cin kujerar dan majalisa daya a jihohin Najeriya da gaza cin kujeran kansila ko daya fadin tarayya
Jam'iyyun da suka rage sune:
Jam'iyyar Accord
Jam'iyyar Action Alliance AA
Jam'iyyar African Action Congress AAC
Jam'iyyar ADC
Jam'iyyar APC
Jam'iyyar ADP
Jam'iyyar APGA
Jam'iyyar APM
Jam'iyyar LP
Jam'iyyar NNPP
Jam'iyyar NRM
Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar PRP
Jam'iyyar SDP
Jam'iyyar YPP
Jam'iyyar ZLP
Jam'iyyar BP
Jam'iyyar APP
A bangare guda, Hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta zabi ranar 19 ga Satumba 2020 domin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo kuma 10 ga Oktoba domin gudanar da zaben jihar Ondo.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 6 ga Febriaru, 2020 a Abuja.
Yace: Wa'adin gwamonin Edo da Ondo zasu kare a ranar 12 ga Nuwamba 2020 da 24 ga Febrairu 2020.
Yace: "Kamar yadda sashe na 178(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, ba za'a iya gudanar da zabe ana saura kwanaki sama 150 da karewar wa'adi ba kuma ba za'a iya gudanarwa kasa da kwanaki 30 ba."
"Saboda haka, hukumar ta zabi ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, 2020 matsayin ranar gudanar da zaben jihar Edo kuma na zabi ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2020 matsayin ranar zaben gwamnan jihar Ondo."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng