Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya

Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya

A yau ne wata mujallar kasar Rasha ta sanar da cewa kasar ta kammala kera wa Najeriya jiragen yaki 7. Za a kawo su nan ba da dadewa ba zuwa kasar Najeriya.

Idan zamu tuna, fadar gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa gwamnati za ta sayo sabbin jiragen yaki daga kasar Rasha domin ta karfafa yakin da take yi da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, miyagu yan bindiga da sauran miyagun laifuka.

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba 2019 yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta ruwaito cewa Garba Shehu wanda yana daga cikin tawagar shugaba Buhari da ta wuce kasar Rasha domin halartar kasashen Afirka da kasar Rasha da zai gudana a birnin Sochi, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai tattauna da shugaban Rasha Viladmir Putin domin sayo ma Najeriya sabbin jirage yaki daga kasar.

Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya
Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya
Asali: Twitter

"Rasha ta kasance abokiya ga Najeriya dake bamu gudunmuwa ta bangaren Soji wajen yaki da yan ta’addan duk da cewa ba wai mun sanyasu cikin maganan yadda ya kamata bane. Don haka wannan ziyara zata bayar da damar daya kamata ga shuwagabannin kasashe biyu su zauna su tattauna musamman game da batun sayan makamai da jiragen yaki.” Inji shi.

Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya
Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya
Asali: Twitter

Malam Garba ya kara da cewa nan gaba kadan gwamnati za ta bayyana cikakken bayani game da da cinikayyar makaman, sa’annan ya cigaba da cewa kokarin da Najeriya a baya don sayen jiragen yakin daga Rasha ya samu tasgaro ne sakamakon takunkumi da kasar Amurka ta sanya wa Rashan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel