Cikin shekaru 3, Gwamnatin Buhari ta kashe N1.7tr kan wutan lantarki - El-Rufa'i

Cikin shekaru 3, Gwamnatin Buhari ta kashe N1.7tr kan wutan lantarki - El-Rufa'i

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe kimanin tiriliya biyu cikin shekaru uku da suka gabata domin inganta wutan lantarki a Najeriya, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya laburta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan taron kwamitin tattalin arzikin Najeriya a Abuja.

El-Rufa'i ya ce lamarin wutar lantarkin Najeriya ya gurbace gaba daya kuma gwamnatin Buhari ba zata iya cigaba da kashe kudi haka ba.

Yace: "Gaba daya sashen (wutan lantarki) ya kareraye, yadda aka sayar da kamfanin wutan ni ciwa da dama tuwo a kwarya. Saboda haka akwai matsaloli da yawa."

"Abinda mukayi ittifaki akai shine akwai babban matsala a samar da wutan lantarki......Gwamnatin tarayya ta taimakawa bangaren wutan lantarki da N1.7 Trillion a shekaru uku da suka gabata kuma ba za'a iya cigaba da hakan ba."

Gwamnan ya ce mafitan da ake kokarin samarwa zai batawa wasu rai amma shine hanya daya tilo da za'a iya magance matsalan.

"Wannan mafita ba zai yiwa wasu dadi ba, ran wasu zai baci amma shine hanya daya tilo na kawo sauyi da dinke barakar bangaren wutan lantarki shine yanke wasu shawari masu wuyan gaske."

Za ku tuna cewa Kwamitin koli na tattalin arzikin kasa (NEC) ya yanke shawarar sake duba yadda kamfanonin da ke raba hasken wutar lantarki (Discos) ke gudanar da harkokinsu a fadin kasa.

Da yake magana da manema labarai bayan kammala taron NEC a fadar shugaban kasa, tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya ce an kafa wani kwamitin wucin gadi a karkashin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, domin sake duba matsayin kamfanonin.

Ya kara da cewa kwamitin zai kunshi ma'aikatan hukumar sayar da kadarorin gwamnati da na hukumar kula da bayar da kwangila a matsayin mambobi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel