Yanzu-yanzu: Mai magana da yawun Kwankwaso, Binta Sipikin, ta koma APC

Yanzu-yanzu: Mai magana da yawun Kwankwaso, Binta Sipikin, ta koma APC

Mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran mazhabar Kwankwasiyya, Hajiya Binta Spikin, ta sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Hajiya Sipikin ta sanar da sauya shekarta ne ranar Laraba, daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Wanna ya biyo bayan sauya shekan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi, daga PDP zuwa APC.

Sipikin ta bayyanawa Premium Times cewa ya koma APC ne saboda matakin da mai gidanta, Sulaiman Bichi, ya dauka na watsi da Kwankwaso da Kwankwasiyya.

Ta kara da cewa ta dade da raba jiha da Kwankwaso tun bayan zaben 2019 amma sai ranar Laraban nan ta alanta.

Sauran jiga-jigan Kwankwasiyyan da suka koma APC sun hada da Aisha Kaita, shugabar matan ODO a Kano, Muhammad Tarauni, tsohon dan majalisa da kuma Idris Bala, shararren mabiyin Kwankwasiyya.

DUBA NAN Najeriya ce kasa mafi fama da rashawa ta 4 a Afrika ta yamma - Bincike TI

Yanzu-yanzu: Mai magana da yawun Kwankwaso, Binta Sipikin, ta koma APC
Yanzu-yanzu: Mai magana da yawun Kwankwaso, Binta Sipikin, ta koma APC
Asali: UGC

Mun kawo rahoton cewa A yau Alhamis ne Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya karba shugaban jam'iyyar PDP na darikar Kwankwasiyya na jihar Kano, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

A yayin ziyarar da suka kai gidan gwamnatin jihar, Gwamna Ganduje ya karbesa tare da sauran shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomi 44 na jihar.

Yayin bikin karbar Bichi tare da sauran jahororin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, Ganduje ya fada musu cewa "wannan jar hula bata dace daku ba."

Da yake mayar da martani ga Ganduje, Rabiu Suleiman Bichi ya ce, "ni kaina na dade ina jin wani irin yanayi a jikina duk lokacin da na sanya jar hula a kaina."

Wannan na kunshe ne a takardar da sakataren yada labarai na Gwamnan, Abba Anwar ya fitar kuma jaridar Solacebase ta samu.

Takaradar ta ce tsohon mai bada shawara na musamman ga Injinay Rabiu Kwankwaso, wasu dalibai da gwamnatin Kwankwaso ta dau nauyin karatunsu, shugabannin jam'iyyu na matakai daban-daban duk sun samu halartar taron da aka yi a gidan gwamnatin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel