Yanzu-yanzu: Mataimakin kakakin majalisar jihar Imo ya yi murabus

Yanzu-yanzu: Mataimakin kakakin majalisar jihar Imo ya yi murabus

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Okey Onyekanma, ya yi murabus daga kujerarsa.

Kakakin majalisar jihar, Collins Chiji, ya bayyana hakan a wasikar da ya karanta a zauren majalisa ranar Talata.

Bugu da kari, Onyekanma ya yi murabus daga kujerar shugaban kwamitin dokokin da kasuwancin majalisar.

Wannan dambarwan siyasan ya biyo bayan hukuncin kotun kolin Najeriya da ta fititiki gwamnan PDP, Emeka Ihedioha, kuma ta baiwa na APC< Hope Uzodinma.

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Dukkan Alkalan kotun kolin sun yi ittifaki a shari'ar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta karanto cewa an zagbewa jam'iyyar APC kuri'un rumfunan zabe 388 yayinda ake tattara sakamakon zaben jihar Imo.

Mai shari'a Kudirat Kekere Ekun tace bayan an hada kuri'un runfuna 388 da aka zabge a farko da kuri'un da yan takaran suka sami, dan takarar APC ya kamata ace hukumar INEC ta sanar matsayin zakaran zaben.

Saboda haka, ta yi watsi da sanarwan INEC na baiwa Emeka Ihedioha nasara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel