Likitoci biyu, marar lafiya daya sun mutu bayan bullar wata sabuwar cuta a Kano

Likitoci biyu, marar lafiya daya sun mutu bayan bullar wata sabuwar cuta a Kano

A kalla mutane uku da suka hada da likitoci biyu ne suka rasa rayukansu bayan barkewar wata cuta da ake zargin zazzabin Lassa ne a jihar Kano.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa anyi wa wata mata mai juna biyu aiki don cire yaro daga cikinta a asibitin koyarwa na Malam Aminu da ke Kano. Matar ta mutu ne sakamakon wani irin zazzabi wanda ake zargin na Lassa ne a makon jiya.

Majiyoyi da yawa daga asibitin sun ce likitan da ya taimaka wajen aikin ya rasu bayan kwanaki kadan da mutuwar mai juna biyun. Hakazalika, wanda yayi wa matar allurai kafin a fara aikin a ICU ya rasu a cikin kwanakin karshen mako.

DUBA WANNAN: Akwai shingen tsare ababen hawa na 'yan Boko Haram a kan hanyar zuwa Maiduguri - Rundunar soji

"Baya ga likitocin biyu da suka rasu, babban likitan da yayi wa matar aiki yana kwance rai a hannun Allah. A halin yanzu an ware shi," wani jami'i da ya bukaci ya boye sunansa ya sanar.

"Asibitin koyarwa na Malam Aminu na kokarin samu sinadarin Ribavirin don amfanin duk wadanda suka taba mai juna biyun. Ana bukatar ma'aikatan lafiya da su kiyaye."

Mai magana da yawun hukumar asibitin, Hauwa Abdullahi bata dau wayar da jaridar Daily Nigerian ta dinga yi mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel