Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kashe shugaban kungiyar CAN da suka sace

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kashe shugaban kungiyar CAN da suka sace

Yan kungiyar tada kayar bayar Boko Haram sun hallaka, Rabaran Lawal Andimi, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya CAN a karamar hukumar Michika, jihar Adamawa.

Yan ta'addan sun yi awon gaba da Lawal Andimi ne a farkon watan a kauyensa.

Dan jarida, Ahmad Salkida, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita da safiyar yau Talata, 21 ga watan Junairu, 2020.

A Ranar Alhamis, 2 ga Watan Junairu, 2019, ‘Yan Boko Haram sun kai hari, har su ka sace babban Faston da ke Kauyen na Michika.

Hakimin Michika, Ngida Kwace, shi ne ya bayyanawa Mai girma Mataimakin gwamna, Crowther Seth, lokacin da ya kawo masu ziyara.

A wani bidiyon da shahrarren dan jarida, Ahmad Salkida, ya saki, Rabaran Andimi ya ce yan ta'addan basu ci zarafinsa tun lokacin da suka saceshi.

Yace: "Ban taba yanke zuciya ba, saboda duk halin da dan Adam ya samu kansa, yana hannun Allah."

"Ina kira ka abokan aikina, rabarori, musamman shugabanmu, Rabaran Joel Billy, wanda babban mutum ne, ya taimaka ya yiwa gwamna Umaru Jibrilla (Fintiri) magana domin a sakeni."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng