Amfanin auren wuri guda 10
Ana yawan cewa aure ba na yara bane. Tabbas ba na yara bane amma na mutane ne masu alkibla wadanda suke kaunar juna kuma suke da burin kasancewa tare har abada. Auren wuri na da amfani masu tarin yawa. Ga kadan daga cikin amfanin auren wuri ga ma’auratan.
1. Ma’aurata zasu girma tare
Idan matasa biyu suka yi aure, akwai yuwuwar su taso tare cike da fahimtar juna da kauna mai tarin yawa har zuwa manyancensu.
2. Ba a cika saka manyan burika ga juna
Idan masoya suka yi auren wuri, basu cika saka burika masu yawa a rayuwarsu ba. Kullum fatansu shine gina rayuwar aure mai kyau tare da taso da yara nagari.
3. Ma’auratan ka saba morar junansu
Sakamakon rashin manyan burika a rayuwa, su kan saba da morar komai na juna. Suna mayar da kayan juna nasu ne.
4. Biki wanda bai cika da karya ba
Sakamakon rashin girman ma’auratan, su kan kwantar da hankali ba tare da sun saka karya ba a yayin shagalin bikinsu.
DUBA WANNAN: Kwadayi: Matashiyar da ta yi lalata da Kare a kan N3m ta samu matsala, tana neman taimako
5. Halayyar amfana da kayayyakin juna
Sakamakon auren wuri, ma’aurata kan saki jiki da juna har su dinga daukar kayayyakin juna suna amfana da ita.
6. Akwai rayuwa mai matukar tsawo
Fara zaman auratayya da wuri kan ba ma’auratan damar doguwar rayuwa tare. Su kan samu isasshen lokacin da zasu zauna har muddin rai.
7. Ma’auratan kan dandana rayuwar manya tun da wuri
Aure kamar yadda wasu suke kallonsa, rayuwa ce ta manya. Auren wuri kuwa na sa ma’auratan su fara dandanar rayuwar manya ta hanyar zama iyaye da wuri.
8. Ma’auratan kan zauna cikin farinciki
Auren wuri na kawo natsuwa da cikar kamala wadanda sune jigo na samuwar farin ciki.
9. Akwai isasshen lokacin rayuwar auren ko kuma kara wani auren idan rabuwa ta gibta
Sakamakon auren wuri, ma’auratan da suka rabu da juna kan kara yin aure da yarintarsu. Basu yi tsufan da zasu ce an hakura da juna.
10. Babu hatsari mai yawa tattare da daukar ciki
Mace mai shekaru 24 zuwa 26 bata tattare da hatsari a yayin da ta samu juna biyu kamar mace mai shekaru 35 zuwa 45.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng