Hargitsi da hayaniya sun tilasta wa CJN ficewa daga zauren kotu ba shiri

Hargitsi da hayaniya sun tilasta wa CJN ficewa daga zauren kotu ba shiri

Babban alkalin Najeriya, Jastis Tanko Muhammad ya fice daga zauren kotu babu shiri sakamakon hargitsi da hayaniya da ta cika babban zauren kotun koli.

Jastis Muhammad, wanda zai jagoranci shari'ar daukaka kara ta gwamnoni bakwai, ya fice daga babban zauren kotun ne sakamakon tsananin cika da mutane suka yi a zauren kotun.

Daraktan shari'a na kotun kolin, Ibrahim Gold ya umarci jama'ar da ba wani takamaiman lamari ya shigo dasu kotun ba da su fice daga zauren kotun.

Ya kara da cewa manyan lauyoyin bangarori da kuma wasu mutane hudu kacal aka amince da su zauna a zauren kotun. "Idan ka shigo ba matsayin lauyan mai kara bane ko wanda ake kara, muna rokonka da ka bar zauren kotun," in ji shi.

A halin yanzu, jami'an tsaro ne ke gyara wajen tare da mayar da zauren kotun yadda za a samu damar shari'ar cikin lumana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel