Tsugune bata kare ba: An fara yi wa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu sabuwar barazana

Tsugune bata kare ba: An fara yi wa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta kudu sabuwar barazana

Wani hargitsi ya kara rincabewa a kasar Afirka ta kudu bayan 'yan yankunan Keimoes da Upington na Arewacin kasar Afirka ta Kudun, a safiyar Alhamis, sun ba 'yan Najeriya da 'yan sauran kasashen duniya sa'o'i 12 da su tattara su bar yankunan.

Adetola Olubajo, shugaban kungiyar 'yan Najeriya dake kasar Afirka ta kudu, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.

Olubajo ya ce wannan cigaban ya biyo bayan mummunan lamarin da ya auku ne tsakanin wani jami'in dan sanda da wani dan Najeriya a ranar Laraba.

Ya ce, an zargi wani dan Najeriyan, kuma dan asalin jihar Ebonyi da sukar dan sanda mai suna Nico Visagie, a yayin da wata hatsaniya ta hada su.

Olubajo ya ce, har yanzu dai ba a samu gamsasshen bayani ba a kan abinda ya hada su daga majiya kwakwara balle a tantance dalilin sukar dan sandan. A halin yanzu kuma yana asibiti kwance a cikin mummunan hali.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta yi 'tir' da kasar Iran a kan kai wa Amurka hari

"Bayan aukuwar lamarin mai bada tsoro, mazauna yankunan Keimoes da kewaye sun fito zanga-zanga tare da kone-konen kadarorin 'yan wasu kasashen, musamman dai 'yan Najeriya," cewarsa.

"Wannan harin yayi kamari inda ya kai ga har an fatattaki 'yan Najeriya da wasu kasashen daga Upington. Daukin gaggawa da 'yan sanda suka kawo a safiyar yau ne ya kwantar da tarzomar amma ba duka ba. Wasu kafafen yada labaran cikin gida sun bayyana cewa, an cafke wasu bata-gari da suka dinga barnatar da dukiyoyin mutane," ya ce.

Ya kara da bayyana cewa, wanda ake zargi da sukar dan sadan na hannun hukuma, kuma za a gurfanar dashi gaban kotu a ranar Litinin mai zuwa ko kafin nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel