Bidiyo: Ni nake safarar bindigu ga 'yan bindiga a jihohin arewa uku - Mai laifi

Bidiyo: Ni nake safarar bindigu ga 'yan bindiga a jihohin arewa uku - Mai laifi

Wani hatsabibin dillalin bindigogi mai suna Samson Salau ya bayyana cewa yana siye da siyar da bindigogi kirar AK-47 ga masu fashi da makami da kuma 'yan bindigar da suka dinga gallabar wasu jihohin Arewa.

A wani bidiyo, Salau ya bayyana hakan ne a harshen Hausa yayin da DSP Hassan Gimba Sule, kwamandan runduna ta musamman ta jihar Neja ke tambayarsa.

Dan asalin jihar Filato din yace, ya fara wannan kasuwancin ne na siye da siyar da miyagun makamai ga masu fashi da makami kusan shekaru uku da suka gabata.

Ya yi bayani yadda yake samo bindigogin daga wani mutum mai suna Zed a Jos.

Kamar yadda yace, "Bayan siyan AK-47 sai in siya harsasai don siyar dasu ga 'yan bindiga da masu fashi da makami dake jihohin Neja, Kaduna, Zamfara da Nasarawa. Ina siyan fisto N90,000 kuma in siyar a N120,000.

"A shekaru uku da suka gabata, na siya kuma na siyar da AK-47 guda dari da fisto 30. Na siya kuma na siyar da kusan alburusai 2,000." ya bayyana.

An kama Salau ne a Minna, babban birnin jihar Neja kuma an kama shi da fisto guda biyu da kuma harsasai 46. Ya yi alkawarin bada hadin kai ga 'yan sanda don bibiya tare da kamo sauran masu siyan hajarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel