Kaduna: IGP ya kara wa 'yan sanda 76 girma

Kaduna: IGP ya kara wa 'yan sanda 76 girma

Kamfanin dillanci labaran Najeriya ya ruwaito cewa an kara wa jami'an 'yan sanda76 girma a jihar Kaduna. Sun hada da DCP uku, ACP goma sha hudu, CSP bakwai da wasu jami'ai 50 dake hukumar 'yan sandan jihar.

"Wannan karin girman anyi shi ne don karfafawa tare da karin kwarin guiwa ga jami'ai masu mayar da hankali wajen aiyukansu. Akwai bukatar ku sauke nauyin da aka dora muku sakamakon wannan karin girman," in ji shi.

Kwamishinan 'yan sandan ya jinjinawa jama'ar jihar tare da kafafen yada labarai a kan cigaba da goyon bayan da suke ba hukumar.

"Wadannan bayanan da koken da suke kawowa ne yake bada nasara ga binciken hukumar," cewar shi.

DUBA WANNAN: Yadda mutane ke hijira zuwa kan duwatsu bayan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

Ya shawarci sauran jami'an da su yi koyi da kyawawan halayyar jami'an da aka kara wa girma wajen sauke nauyin dake kansu.

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyaanwa jami'an da aka kara wa girma cewa, nauyi ne ya hau kansu kuma su shirya fuskantar kalubale.

Ya kara da cewa, aiyukan 'yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma sauran kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta duk sun ragu a jihar.

"Mun yi alkawarin dagewa a wannan shekarar; zamu kuma maye gurbin jami'an da aka kara wa girma da wadanda suka dace. Za a canza musu wuraren aiki", ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel