Kano ta dara London sanyi - NIMET

Kano ta dara London sanyi - NIMET

Yanayin sanyi a garin Kano ya yi kasa zuwa ma'aunin Celcius 8, kasa da na London da ke ma'aunin Celcius 11 a daren ranar Alhamis 2 ga watan Janairun 2020.

Iskar mai karfi tare da sanyi na ranar Laraba da Alhamis ya tilastawa mutane da dama zama a cikin gidajensu kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Hukumar nazarin yanayi ta Najeriya, Nimet ta yi hasashen cewa za cigaba da samun iska mai dauke da kura da sanyi a sassa da dama na kasar a ranar Jumaa.

Hasashen yanayin na Nimet da ta fitar a ranar Alhamis a Abuja ya kuma ce akwai yiwuar samun buji a biranen da ke kusa da teku.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a gidan David Mark a Benue

"Ana sa ran samun iska tare da kura a mafi yawancin jihohin arewa tare da yanayin sanyi na ma'aunin celcius 24 zuwa 32 da rana da ake ran zai sauka zuwa 11 zuwa 6 da dare.

"Jihohin da ke tsakiya kamar Yola, Gombe, Bauchi, Zaria, Kaduna da Jos ana sa ran samun matsakaicin kura tare da yanayin garuruwan da rana za su kama daga 25 zuwa 36 a mau'aunin celcius sannan da dare kuma su koma 10 zuwa 17," inji rahoton.

A cewat Nimet, za a samu iska da matsakaicin yanayi a jihohin da ke kudancin Najeriya wadanda ba su kusa da teku.

Hasashen ya nuna cewa za a samu yanayin celcius 26 zuwa 36 da rana sai kuma dare 14 zuwa 21.

Mutane da dama sunyi mamakin irin yadda sanyin da iskar na wannan shekarar ya zo da karfinsa sosai idan aka kwatanta da na bara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel